Ban taba tara biliyan 1 a asusun bankina ba —Ngilari
Tsohon gwamnan ya ce bai taba tara makudan kudaden da ake zarginsa da su ba.
Tsohon Gwamnan Jihar Adamawa, Bala Ngilari, ya ce bai taba samun kudin da ya kai Naira biliyan daya a asusunsa na banki ba a lokacin da yake kan mulki.
Ngilari ya bayyana haka ne a ranar Laraba a shirin gidan talabijin na Channels, inda ya ce ya bayyana hakan ne don kare kansa daga wani zargi da ake masa.
- Tare muka kammala jami’a da Tinubu a Amurka —Ogunsanya
- ’Yan Najeriya 936 sun rasu a hatsarin kwalekwale a shekara 3
“Za a iya tantance wannan, za a iya duba asusuna, shekaru takwas da suka wuce – babu lokacin da na taba samun Naira biliyan daya a cikin asusuna,” in ji Ngilari.
A cewar tsohon gwamnan, ya samu damar da zai iya tara irin wadannan kudade, amma hakkin da ya rataya a kansa ta fuskar shari’a sun bude masa hanyar da ya dace wajen sarrafa kudaden jihar.
“Wannan ba yana nufin ban samu damar da zan samu irin wadannan kudaden ba lokacin da nake gwamna. Wannan ba shi ne hanyar da na zaba wa kaina ba, kuma na lura cewa ni lauya ne – Na dade ina bin doka.”
Tsohon gwamnan ya yi ikirarin cewa kalaman da ya yi a baya wasa yake, amma mutane sun dauki batun da muhimmanci.
Da yake karin haske, Ngilari ya ce ya yafe wa wadanda suka bayar da gudummawa wajen yanke masa hukunci biyo bayan wata shari’ar rashawa da Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati (EFCC) ta shigar a kansa.
Ya kuma kara da cewa ba zai kara yin magana a kan batun ba.
Ngilari, wanda ya rike mukamin gwamnan jihar, daga watan Oktoba 2014 zuwa watan Mayu 2015, an same shi da laifin almundahanar Naira miliyan 167, aka yanke masa hukuncin dauri bayan ya bar mulki.
EFCC ta tuhume shi ne da laifin karya dokokin sayen kaya, wajen bayar da kwangilar Naira miliyan 167 ga kamfanin El-Yadi Motors Limited na samar da motoci guda 25 (Toyota Corolla).
Wata babbar kotu da ke zamanta a Yola, babban birnin jihar Adamawa ta yanke masa hukuncin daurin shekaru biyar, amma daga baya kotun daukaka kara da ke Yola ta sallame shi kuma ta wanke shi.