Ban taba tunanin tsayawa takarar shugaban kasa ba-Osinbajo
Mataimakin Shugaba Kasa, Yemi Osinbajo wanda ya taba rike mukamin mukaddashin shugaba kasa ya ce bai taba tunanin tsayawa takarar shugabancin kasar nan ba a zabe mai zuwa. Rashin tabbas na ko Shugaba Muhammadu Buhari zai sake tsayawa takara karo na biyu ya janyo kace-nace a kasar. Osinbajo dan kimanin shekaru 60 a duniya ya […]

Mataimakin Shugaba Kasa, Yemi Osinbajo wanda ya taba rike mukamin mukaddashin shugaba kasa ya ce bai taba tunanin tsayawa takarar shugabancin kasar nan ba a zabe mai zuwa.
Rashin tabbas na ko Shugaba Muhammadu Buhari zai sake tsayawa takara karo na biyu ya janyo kace-nace a kasar.
Osinbajo dan kimanin shekaru 60 a duniya ya rike mukamin mukaddashin shugaban kasa lokacin da Buhari yake jinya a kasar Ingila inda ya rage fargabar da ake da ita a yankin Neja Dalta mai arzikin man fetur tare da bunkasa harkokin kasuwanci.
Hakan ya sanya wadansu ke ganain idan ya zama shugaban kasa zai iya gyara tattalin arzikin kasar.