Ban taba tunanin zama Sarki ba —Sarkin Bichi
Muhimman abubuwan da za ku so sani kan Sarkin Bichi, Alhaji Nasir Ado Bayero.
Alhaji Nasir Ado Bayero shi ne Sarkin Bichi, daya daga cikin masarautun da aka kiriro a baya-bayan nan a Jihar Kano. Kuma kanen Mai martaba Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero ne, dukkansu ’ya’yan marigayi Sarkin Kano, Alhaji Ado Bayero.
A wannan tattaunawa ta musamman, Sarkin Bichin ya bayyana yadda ya taso da dangantakarsa da Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II; da yadda yake hada aikinsa na Sarki da harkar kasuwanci.
Ya kuma yi tsokaci kan abin da ya shafi rashin tsaro da tashe-tashen hankali da suka addabi kasar nan hade da gudunmawar da sarakuna suke bayarwa wajen dakile fitinu.
Sarkin ya kuma yi magana game da alakarsa da ’ya’yansa, inda daya daga cikinsu, Zahra za ta auri dan Shugaban Kasa Muhammadu Buhari, Yusuf a ranar Juma’a, inda ya ce ya so a ce ta kammala makaranta kafin ta yi aure:
Mai martaba, ko za ka iya fada mana yadda ka girma a cikin gidan sarauta, ma’ana kadan daga cikin farkon rayuwarka da kuma irin dabi’un da ka samu daga mahaifinka?
Watakila ba lallai ba ne in iya tuna komai game da farkon rayuwata ba. Amma zan iya tuna cewa na taso ina da kusanci sosai da mahaifina.
A matsayina na saurayi a cikin fadar, a zahiri na girma kusa da shi. Zahiri, na girma a gadonsa.
Na taso tare da shi har zuwa lokacin da na fara karatu a makarantar sakandare.
Zan iya tuna akwai wasu lokuta da nake makarantar firamare lokacin da nake buya in gudu kan gadonsa in yi barci.
Nakan taimaka masa wajen daura rawaninsa. Don haka, na san shi sosai.
Wannan shi ne tushen ilhamar da na samu a rayuwata daga mahaifina.
Ba a taba dauka ta a matsayin wani yarima ba. Na taso tare da bayi a fada, da ni da sauran yara ba wani bambanci. Ban taba samun wata alaka ta musamman ko wata kulawa ta musamman ba kuma hakan ya yi tasiri sosai game da halayena a yau.
Ka girma a matsayin wanda ya shahara a cikin gidan sarauta, shin hakan yana da alaka da kusancinka da mahaifinka ko kuwa yana da alaka da hanyar da kuka taso, misali kamar yadda ka ambata, ka taso tare da kowa a ciki fadar, wanda muka sani cewa ita fadar babban gari ne a karan kanta?
Zan iya cewa duka biyun ne. Na kasance kusa da shi. Nakan ji ba dadi a raina duk lokacin da na tuna da shi.
Na rayu a duniya kamar kowa kuma ba na ji na a matsayin wani na musamman har yanzu. Ina tsammanin wannan shi ne asalin.
Lokacin da mutane ke fada min cewa ni Yarima ne, abin yakan yi min wuyan gaskatawa. Na san ina da rawar da zan taka sannan na fara jin haka a jikina. Iyakar abin da zan iya tunawa ke nan.
Shin kana da wani tunani don koyi da tsarinsa ba wai kadai don zama sarki ba har ma wasu fannoni na rayuwa?
Ya kasance abin koyi gare ni koyaushe. Don haka, zama Sarki wani abu ne na daban, amma dangane da halaye da dabi’u da abin da yake yi, koyaushe ina bin sa don ganin abin da yake yi domin in koya kuma hakan ya taimaka min sosai.
Mahaifinku, Allah Ya ba shi damar yin mulki na dogon lokaci kuma ya shahara sosai ba a Kano kawai ba har ma a wajen kasa da duk inda ya je. Sannan lokacin da rasuwarsa ta zo wanda ba makawa, mutane da yawa sun yi tunanin za ka gaje shi. Yaya ka ji lokacin da haka ba ta kasance ba?
Nufin Allah ne. Haka Allah Ya so. Ban taba tunanin zan zama Sarki ba. Bai taba zama wani buri a wajena ba.
Haka ne, ina son in yi nasara. Tabbas, ina son in zama mutum mai nasara amma ba ni da burin zama Sarki ko hakimin gunduma ko wani abu.
Ina so in yi wani abin a-zo-a-gani a rayuwata. Ka aikata wa mutane alheri don ci gaba. Don haka, kasancewar ni ba Sarki ba ne lokacin bai sa ni jin wani bambanci ko bakin ciki ba, ko kadan. Nufin Allah ne ba wanda zai iya canja haka.
Yaya ka ji lokacin da aka nada ka Sarkin Bichi?
Yanayin ya kasance iri daya kamar yadda nake ji a baya. Tabbas kamar yadda na ce, ina son rayuwa cikin natsuwa.
Za a ji kamar wani iri in ce, na girma a cikin gidan sarauta amma kuma ina son rayuwa ni kadai, wannan shi ne matsayata.
Don haka, sake zama Sarki a yanzu a wannan lokaci nufi ne kawai na Allah, kawai dama ce na yi aiki don yin hidima ga al’umma.
Yaya kake ji game da sha’anin mulki a wannan dan lokaci da ka dauka a kan mulki? Yaya kake ji game da kalubalen, ko dadi game da haka, idan aka hada da rayuwarka ta yau da kullum?
Ina tsammanin na girma a kan haka. Don haka, a gare ni kawai kari ne a kan abin da nake yi a da.
Koda a matsayina na Yarima za ka iya cewa rayuwata ta zama gaba daya don hidima ga mutane.
Dama tun lokacin da na san kaina a matsayin saurayi, ko da nake a matsayin Yarima, ko shugaban gunduma.
Don haka, wannan ci gaba ne kawai na rayuwa kuma babu abin da ya ruda ni; da wannan, ina nufin don cewa na zama Sarki, al’ada ce a gare ni.
Na kasance kamar da, ba na jin wani iri daban, ba na jin nauyin hakan, ba na jin wata gajiyawa, na gode wa Allah ina jin dadi.
Yanzu, za a yi bikin bayar da sandar sarauta kuma haka ya zo, za a yi shi tare da bikin auren ’yarka. Yaya abin yake ga jama’a?
Duk mun kasance cikin yanayin farin ciki, yanayin shiri; akwai abubuwa da yawa da za a yi.
Muna kan shirin haka don haka tabbas muna neman taimakon kowa ciki har da ku ’yan jarida.
Don haka, ina tsammanin za mu yi lafiya kuma ai magana ce ta biki da kansa, magana ce ta ci gaba, irin karfin gwiwar da muke da shi a kan mutane; ikon jawo hankalinsu da kuma canja rayuwarsu da sanya su farin ciki gwargwadon ikonmu.
Don haka, bikin a gare ni, babban abu ne don ina jin ina ma zan iya jawo bikin a yi da sauri kuma in ci gaba da harkokina.
Ranka ya dade, za a iya kiyasta yadda wannan al’amari zai kasance. Ba da sandar girma hade da daurin aure musamman ma a ce ’yarka za ta auri dan Shugaban Kasa. Na san cewa ka halarci manyan tarurruka irin wadannan, amma yaya kake jin matsayin wannan na auren ’yarka?
Ban san yadda zan misalta irin wannan farin cikin ba, amma sai dai rabuwa da ’ya abu ne marar dadi.
Na shaku da ’ya’yana, saboda rabuwa da Zahra wani babban al’amari ne a wajena, sai dai muna godiya ga Allah.
Yarinya matashiya ’yar shekara 20 wanda yanzu haka tana shekarar karshe a jami’a tana karatu a kan harka ilimin fasahar zanen gine-gine.
Na so a ce Zahra ta gama karatunta. Mun dan yi rayuwa da ita na dan wani lokaci, sai dai ba za mu iya canja abin da Allah Ya kaddara ba. Muna musu fatar alheri da rayuwa mai albarka.
Tabbas kuma wannan lokaci ne na farin ciki a wajena. Na riga na aurar da wata ’yar tun watan Janairun bana, kuma ga shi ma zan aurar da wata in Allah Ya yarda.
Kamar yadda Manzon Allah (SAW) ya ce duk wanda ya yi tarbiya kuma ya aurar da ’ya’yansa mata guda uku Allah zai yi masa tanadin gida a Aljanna; Wannan shi ne fatata kuma ina addu’a cewa ta hanyarsu Allah zai ba ni Aljanna.
Bari mu sake dawowa maganar fada, yaya alakarku take da dan uwanka, Sarkin Kano?
Dan uwana ne na jini. Uwa daya ce ta haife mu. Yaya kake tunanin mutum zai ji a kan haka?
Dangantakarmu aba ce babba kuma tare muka taso. Kusan ya girme ni da tsawon shekara uku.
Saboda haka muna da dangantaka mai karfin gaske kuma muna ba wa juna sharawa a kan abubuwa idan suka taso. Mun gama da sha’anin kuruciya yanzu mun zama masu zartarwa.
Rayuwar sarauta ta dan bambanta da rayuwa ta yau da gobe a wajen gari. Yanzu kun zama sarakai, shin kuna samun damar aikata wasu abubuwa irin da, kamar samun damar tattaunawa ta daban saboda za ka ga duk inda za ku je jama’a suna tafe tare da ku?
Kusan hakan ba ya yiwuwa. Har yanzu ina tuna wadannan lokutan da kawai za ka fita ka tuka motarka ka tafi inda kake so, ka samu jin dadi, ka yi tafiyarka da kafa.
Yanzu duk abubuwa sun canja, amma nakan dan gwada idan na samu dama.
Wasu lokuta nakan so in zauna da abokaina mu tattauna kamar yadda muka saba.
Sai dai yanzu aiki ya shiga tsakani, sai ka zauna ka fara tattaunawa da abokanka sai ka ji an ce ga wata matsala a wani waje, ga wani aiki a wani waje, ga wani bako yana jira. Abin dai babu hutu.
A wasu lokuta da dama idan na yi tafiya daga nan Kano zuwa Bichi, wani lokacin a ranar da ba ta aiki ba, ba na iya samun hutu, ko na sakan daya saboda karbar gaisuwa.
Akwai abubuwa da yawa da mutane suke son ka yi musu, babu kuma yadda za ka yi sai ka yi musu.
Kirkiro sababbin masarautu ana ganin kamar ya kawo rabuwar kai a Kano da wajenta, kuma ya jawo ka-ce-na-ce a kotuna. Yaya alakarku yanzu take da sauran masu sarauta wadanda suka soki wannan tsari wadansu ma yanzu suna karkashin ikonku da sauran masarautu, duk da cewa kun kasance tare na wani tsawon lokaci?
Ban ga wata alama ta kyama ba, yadda na dauka shi ne ba za mu taba canja abin da Allah Ya kaddara ba. Ko kana so, ko ba ka so, ba za ka taba iya canjawa ba.
Game da alakarmu kuwa, ban taba samun wata matsala da wani ba a kan haka, ta zamantakewa ko kuma ta bangaren aiki.
Saboda haka zan iya cewa ban da wata matsala tun daga zamana hakimi har zuwa zamana sarki ban taba samun cikas ba.
Kuma yaya abin yake ta bangaren zartarwa a tsakanin wadannan masarautu, ko a ce a tsakanin masarauta da masarauta ko kuma Majalisar Sarakuna ta Jihar Kano?
Har zuwa yanzu ba a kaddamar da Majalisar Sarakunan ba. Saboda haka muna aiwatar da ayyukanmu a tsakaninmu, ta namu bangaren.
Idan akwai wani batu da ya faru a wani waje kamar harkar sulhu a tsakanin jama’a, kamar a ce a Rano ko a Kano, muna da hanyar da muke sadarwa a tsakaninmu.
Muna haka a koyaushe. Idan aka samu wani ya kawo kara a kan wani abu da yake da alaka da Fagge amma sai ya zo Bichi, ina da hanyar da zan mai da shi zuwa ga Sarkin Kano.
Saboda na ga yadda mahaifina yake lokacin na taso, idan aka samu wani batu kamar a ce daga Zariya na ga yadda yake mayar da wannan batu zuwa wurin da ya dace.
Saboda haka muna tafiyar da aikinmu yadda ya dace, idan a kan batun jihohi ne kuma muna da hanyar da muke tattaunawa wajen warware matsala.
Mai martaba, ga shi ka dade a kan karagar mulki tsawon wani lokaci, kuma kamar yadda yake a fili ka dade a gidan sarauta, ka kasance hakimin kanana hukumomi da dama kuma ka ga abubuwa da dama a Najeriya, sai dai yanzu a kasar nan abubawa da dama suna ta faruwa musamman ta fuskar tsaro. Sai dai alhamdulillahi a Kano muna cikin zaman lafiya fiye da sauran wurare, wace gudunmawa kake tunanin za ka iya bayarwa don tabbatar da zaman lafiya ta yadda hakan zai yi tasiri ga sauran bangarorin kasar nan?
Idan ka ce na ga abubuwa da dama sai in ji kamar wani tsoho da ya dade sosai.
Ban ga abubuwa da yawa ba (dariya). Ai tuntuni muna aiki a kan haka wajen samar da zaman lafiya.
Babban abin shi ne, ta hanyar ba da labarai idan wani abu ya faru.
Mu sarakuna muna da hanyar tattara bayanai, wannan hanyar tattara bayanan ita ta sa muke da muhimmanci.
Idan ina so in samu wani labari kamar a ce a Bagwai, zan samu bayanan cikin minti biyu.
Kawai hanya ce ta tattara bayanai, basirar da muke amfani da ita wajen aikata haka ta sha bamban, tun daga unguwanni zuwa karamar hukuma har zuwa masarautu.
Masu sarautunmu suna kawo mana rahoto game da abin da yake faruwa a kowace safiya.
Idan muka samu labarin wani bako ya shigo, za mu samu wannan bayani a wannan safiyar cewa akwai bakin makiyaya sun shigo sun zauna a wani waje.
Mai unguwa zai je ya samo bayanan a kan dalilin da ya sa suka zo wajen, kuma mene ne matsalarsu.
Zai kuma sa ido ya ga me suke aikatawa a wajen. Sannan su kawo mana bayanai mu kuma mu gaya wa gwamnati, har zuwa ga ’yan sanda. Wannan shi ne abin da za mu ci gaba da yi wa gwamnati. Tabbas ina ganin hakan yana ba da gudunmawa da taimakon Allah.
Mutane suna cewa Mai martaba mutum ne mai yawan zirga-zirga. To yaya kake yi tsakanin tsarin rayuwarka da kuma wannan sabon matsayi?
Ina ma a ce na san bambancin, ni kawai ina rayuwata ce ba ni da matsala game da hakan.
Sau da dama idan ina wasu abubuwa da suka shafe ni, ni kadai sai kuma wasu abubuwa su bullo, kuma nakan warware su.
Idan na warware su hakan yakan shafi sauran wasu abubuwa.
Na gode wa Allah cewa ina da kwararau masu taimaka min. Suna iya kokarinsu su ga cewa duk abin da zan aikata na yi daidai. Ina da kwararrun hakimai, ina da hukuma mai karfi.
Na gode wa Allah domin sun kasance kashin bayana. Duk inda zan tafi, koda zan yi tafiya in bar Bichi in je duk inda nake so ba za su kware min baya ba. Wannan shi ne babban abin da yake kara min kwarin gwiwa.
Wannan tambayar ta shafe ka kai kadai. Wasu abubuwa ne Mai martaba ya fi so kuma wadanne ne kasa da haka?
Da farko dai ina son zama ni kadai. Nakan ji dadi in bar cikin mutane in kasance ni kadai, idan na samu damar aikata haka. Yin haka yana ba ni damar in duba abubuwan da na aikata, in duba in ga me ya kamata in aikata nan gaba.
Amma idan kana cikin mutane yana da wuya ka iya yin irin wannan tunani.
Amma idan kana zaune kai kadai za ka iya kirkiro abubuwa, za ka samu damar gyara kuskurenka kuma ka samu damar gano abin da ka aikata.
Ni a wajena haka wata dama ce ta yin nazari kuma ina son aikata haka a kullum. Ina so in zauna ni kadai.
Ina son karatu. Ni mutum ne mai shaukin karatu. Ina karanta littattafai. Ina karanta duk littafin da na samu. Ina matukar karatu, duk inda na je sai ka same ni da littafi, har lokacin barci ina tare da littafi.
Ina son tafiye-tafiye. Duk da cewa tafiye-tafiye yanzu sun zama abin da suka zama. Amma tabbas ina son tafiye-tafiye. Idan na samu dama nakan so in yi tafiye-tafiye in zauna ni kadai.
Idan na samu hutun aiki, nakan kuma yin tafiya da kafa, wannan dabi’ar na samo ta ce daga wajen mahaifina.
Wani lokaci idan muka yi tafiya ni da mahaifina mukan yi tafiya da kafa har na tsawon sa’a biyu ko uku.
Idan muka gaji sai mu samu waje mu zauna don mu huta, idan muka sha ruwa sai mu tashi mu ci gaba da tafiya.
Har yanzu ina yin irin wannan tafiya da kafa idan na samu lokaci. Idan na je Legas na san zan samu dama, a can nakan gwada yin haka.
Tambayata ta gaba, wasu abubuwa ne kasa da haka?
Ba zan iya tunawa kai-tsaye kan abubawan da nake so kasa da wadannan ba.
Da ka yi maganar tafiye-tafiye tare da mahaifinka, sai na tuna lokacin da na gana da Alhaji Aminu Dantata a bara, ya fada min adadin kasashen da ya ziyarta kuma ya ce yawancin tafiye-tafiyen da ya yi tare da mahaifinka ne, ban sani ba ko za ka iya tuna adadin kasashen da kuka ziyarta?
Ba zan iya tunawa ba kaitsaye, sai dai zan iya tuna cewa na zayarci kasashe sama da 100 a fadin duniya. Na yi tafiye-tafiye sosai.
Matsalar rashin tsaro da muka tattauna a baya yanzu tana haifar da kiraye-kirayen sake fasalin kasa da tayar da zaune-tsaye a wasu sassan kasar nan kuma akwai wadansu mutane a Arewa wadanda su ma suke bayyana damuwarsu game da wannan lamari. Mece ce shawararka ga shugabanni da sarakuna kan yadda za a hada kai a magance wannan lamarin?
Ina ganin idan muka yi amfani da albarkatunmu, muka yi aiki a matsayinmu na ’yan kasa daya zai fi kyau a kan cewa a rabu.
Mun ga yadda kakanninmu suka yi fafutika don ci gaban hadin kan Najeriya.
Mun ga yadda wadansu daga cikinsu suka mutu a kan kokarin yin hakan.
Mun ga yadda wasu kasashe suka shiga cikin rudani don rarrabuwar kawunansu saboda wasu dalilai na son zuciya.
Don haka, gara mu zauna tare a matsayin kasa daya. Ba zan iya tunawa da abubuwa sosai game da Yakin Basasa da ya faru ba, amma mun ga wasu kasashe kamar Rwanda, duk da cewa Rwanda ta shawo kan matsalarta, amma ka kalli Sudan.
Kudancin Sudan sun tayar da kayar baya sama da shekara 20 don su raba kasar. Dubi abin da ya same su yau.
Sun samu ’yancin kan nasu, shin sun samu yadda suke so? Shin sun fi wadata a yanzu? Ko kuma yakin ya kare? Bai yiwu ba.
Ya kamata mu yi kira ga mutane mu nemi hanyar da ta fi dacewa don warware matsalolinmu cikin lumana maimakon raba kanmu.
Kamar yadda na fada game da Sudan, na je Darfur a baya na ga yadda abubuwa suka zama.
Yanzu hatta Kudancin Sudan, kamar yadda ake kira yau sabuwar Sudan, har yanzu tana cikin rudani.
Za mu so mu ci gaba da kasancewa cikin hadin kai a Najeriya. Mun san akwai batutuwa amma za mu iya warware su a siyasance.
Za mu iya warware su a cikin gida a matsayinmu na ’yan kasa daya, ba tare da mun yanke shawarar raba kasarmu ba.
Mai martaba, mutane da yawa sun ce akwai abubuwa da suke siffanta ku tare da tsohon Sarkin Kano, Muhammadu Sunusi II, kamar fasahar rayuwa, kamar yadda ka ambaci tafiye-tafiyenku zuwa kasashe daban-daban kuma kuna da abokan tarayya a duk fadin kasar nan. Ta yaya yanzu kuke haduwa (da shi) ban da dangantakar dangi wadda tabbas tana nan. Har yanzu akwai wannan alakar da tsohon Sarkin?
Tabbas! Mun girma tare a gado daya a zahiri. Ya girme ni watakila na kusan shekara uku amma mun kasance abokai tun daga farkon rayuwa. Mun girma tare.
Ya koma fada inda nake, dakina karamin dakina. Muna zaune tare da shi. Muna karin kumallo tare sannan ma muna yawan fita tare. Tare muka rayu da shi, don haka har yanzu muna da alaka.
Mu abokai ne, mu dangi ne kuma a cikin dangin da muka girma mun kasance mafiya kusanci da juna.
Abokantakarmu ta kasance abar buga misali a cikin fada saboda iyayenmu ma tare suka girma.
Marigayi Ciroma Aminu Sunusi da mahaifina ma manyan abokai ne kuma mahaifina kawunsa ne (Sarki Sunusi). Na’am! Har yanzu muna da kyakkyawar alaka mai kyau.
Daga Naziru Mika’ilu da Clement A. Oloyede da Lubabatu Garba da Muhammad Sulaiman