Ban taba tunanin zan yi tashe kamar haka ba —Azeema

Hira ta musamman da tauraruwar fim din Gidan Badamasi, Hauwa Ayawa

Ban taba tunanin zan yi tashe kamar haka ba —Azeema

Jarumar fina-finan Kannywood Hauwa Ayawa, wacce aka fi sani da Azeema a fim din Gidan Badamasi, ta ce ba ta taba tunanin za ta yi tashe kamar haka ba a rayuwarta.

Jarumar ta bayyana haka ne ga wakilinmu da ya samu tattauna da ita. Ga yadda hirar ta su ta kasance:

Ko za ki fada mana wace ce Azeema?

Suna na Hauwa Ayawa, amma an fi sani na da a masana’antar shirya fina-finai da Azeema; Na samu wannan suna ne sakamakon sunan da na fito da shi a Gidan Badamasi da ake haskawa a tashar Arewa24.

An haife ni a jihar Kaduna kuma a nan na yi karatun firamare, daga baya na tafi jihar Zamfara inda a nan na yi karatun sakandire a Makarantar Sakandaren Mata ta Gwamnatin Tarayya da ke Kwatarkwashi.

Bayan kammala sakandare kuma na halarci makarantar koyon ilimin kwamfuta, a yanzu kuma ina shirye-shiryen tafiya makarantar gaba da sakandare domin karatu mai zurfi.

Ya aka yi kika shiga harkar fim?

Dama dai mahaifiyata furodusa ce, to tun ina yarinya na taso da sha’awar fitowa a matsayin jarumar fim. Na taso ina ganin jarumai da dama a gidanmu.

A karon farko an gabatar da ni ga daya daga cikin fitattun daraktoci a masana’antar, Muhammed Alfa Zazi, wanda shi ne ya fara sani a harkar wasan kwaikwayo a Kannywood kuma tun a wancan lokacin ya zama na shiga harkar tsundum.

To cikin wannnan hali ne wata rana ana cikin shirya wasa na hadu da Falalu Dorayi mai ba da umarnin fim din Gidan Badamasi, sai ya yaba da irin yadda na ke gudanar da wasan.

Sai ya yi min tallar fitowa a sabon shirinsu na Gidan Badamasi kuma shi ke nan daga nan sai na fara fitowa a matsayin Azeema daga nan kuma aka sa min suna Azeema.

Wane yanayi ki ka tsinci kanki a karon farko?

A gaskiya na yi mamakin yadda na taka rawa a fitowata ta farko, don hatta abokanan aikina sun sha mamakin yadda na yi ‘acting’ din ba tare da matsala ba, kamar wacce dama ta kware a harkar, saboda na yi komai yadda ake so ba tare da wata matsala ba.

Wane fim kika fara fitowa a rayuwarki?

Musaddiq shi ne shirin da na fara fitowa a rayuwa. Mustapha M. Sharif shi ne wanda ya bayar da umarnin shirin kuma shi ne shirin da ya sa aka sa ni a cikin shirin Karar Kwana kuma wadanan fina-finan sun sa masu shirya fina-finai samun karfin gwiwa a kaina.

Yanzu a cikin fina-finai nawa kika fito a rayuwarki?

A gaskiya ba zan iya fadin fina-finan da na fito a ciki ba yanzu, sai dai nasan na fita a fina-finai sama da 25.

Wace rawa kike takawa a cikin shirin Gidan Badamasi?

A cikin shirin na fito a matsayin ’yar autar Alhaji Badamasi, matsolon mai kudin da ba a cin kudinsa, kuma duk da cewa Falalu shi ne mai ba da umarnin shirin amma kuma ya fito a matsayin mai gadi.

A cikin shirin na fito a shalelen alhaji, wadda alhaji yake kauna, wannan ya sa su ma ’yan uwana suma suke so na.

Kina jin dadin abin da magoya bayanki ke fadi game da yadda kike fita a shirin?

Sosai ma kuwa, abin yana burge ni, saboda ban taba tsammanin za a san ni a wannan dan kankanin lokacin ba.

Amma idan ana magana akan irin rawar da nake takawa a cikin shirin sai ka tsammani na dade a cikin harkar, to ba abin da zance sai godiya ga Allah.

Wane abu ne ba za ki taba mantawa da shi ba a harkar fim?

To abin da bazan taba mantawa da shi ba shi ne kyautar turare da wani karamin yaro ya yi mani.

Yaron karami ne sosai amma yana so na sosai, bayan mun hadu da mahaifiyarshi ta shaida min yadda yaron yake goyon bayana sosai duk da bai taba gani na a gaske ba, kuma ranar da muka fara haduwa da shi shi ne ya roki mamansa ta ba shi turare ya ba ni, ba zan taba mantawa da wannan ba.

A jikin kwalbar lemon Pop Cola mun ga hotonki ko za ki fada mana ya akai aka saka hoton naki?

Hmm! Wannan yana daga cikin abubuwan da bazan taba mantawa da su ba a harkar fim.

Yana daga cikin abun da idan na tuna suke faranta min rai.

Ban taba tunanin za a zabe ni ba lokacin da kamfanin suka nemi wadanda za su sanya a jikin kwalbar tasu ba, kwatsam kawai sai na ji an zabe ni tare da sanannun mutane irinsu Ahmed Musa. Na ji dadin hakan sosai.

Shin kin taba nadamar tsintar kanki a Kannywood?

Ko kadan ban taba nadamar tsintar kaina a Kannywood ba, kuma ina farin cikin kasncewa a wannan masana’antar musamman ganin yadda nake bayar da irin tawa gudummawar ga al’umma.

Shin ya maganar soyayya ko auren Azeema?

A’a, a halin yanzu abin da na mayar da hankali a kai shi ne sana’ata da kuma yadda zan gina kaina ko da bayan na daina harkar fim.

Ina son zama mai shirya fim idan na daina fitowa a matsayin tauraruwa, to don haka abin yana bukatar a shirya masa.

Kuma a matsyina na mace na san wata rana dole zan yi aure. Idan lokacin ya yi zan yi.