Ban tilsta wa jama’a Pwajok takarar Gwamnan Filato ba – Gwamna Jang

Gwamnan Jihar Filato Mista Jonah Jang ya musanta zargin da ake yi masa cewa shi ne ya dora wa al’ummar jihar dan takarar Gwamna na Jam’iyyar PDP Sanata GNS Pwajok.  Gwamna Jang ya musanta wannan zargi ne a lokacin da yake jawabi a wajen yakin neman zabenGwamna na PDP da aka gudanar a garin Angware […]

Ban tilsta wa jama’a Pwajok takarar Gwamnan Filato ba – Gwamna Jang
Ban tilsta wa jama’a Pwajok takarar Gwamnan Filato ba – Gwamna Jang

Gwamnan Jihar Filato Mista Jonah Jang ya musanta zargin da ake yi masa cewa shi ne ya dora wa al’ummar jihar dan takarar Gwamna na Jam’iyyar PDP Sanata GNS Pwajok. 

Gwamna Jang ya musanta wannan zargi ne a lokacin da yake jawabi a wajen yakin neman zaben
Gwamna na PDP da aka gudanar a garin Angware da ke karamar Hukumar Jos ta Gabas.
Ya ce, “Na ji ana cewa wai ni ne na dora wa al’ummar Filato, GNS Pwajok a matsayin dan takarar kujerar Gwamnan Jihar Filato a karkashin Jam’iyyar PDP kan dole, masu wannan magana karya suke yi.”
Ya ce kowa ya gani a wajen da aka gudanar da zaben fidda-gwani, wakilai masu zabe na Jam’iyyar PDP su ne suka zabi GNS Pwajok a wannan takara da yake yi. Kuma wadannan
wakilin PDP da suka zabi GNS Pwajok sun fito ne daga kowane bangare na Jihar Filato.
Gwamna Jang ya ce amma abin takaici sai ga wadannan mutane sun zo suna ta karyar cewa wai don shi Berom ne. “Ni Jonah Jang na dauko shi na dora shi a kan al’ummar Filato dole,” inji shi.
Gwamna Jang ya ce Jam’iyyar PDP ba ta bai wa al’ummar Jihar Filato kunya ba, domin a cikin shekara takwas na mulkinsa sun gudanar da ayyukan raya kasa da dama a jihar. Ya ce babu shakka idan aka zabi GNS Pwajok a matsayin Gwamna zai ci gaba da gudanar da irin wadannan ayyuka na raya kasa a jihar.
A jawabin dan takarar Gwamna na PDP, Sanata GNS Pwajok ya ce a yanzu Allah Ya riga Ya hada kan al’ummar Jihar Filato, kuma ya ce da yardar Allah irin miyagun abubuwan da suka faru a baya a jihar ba za su sake faruwa ba.
Ya ce “Mu matasan Jihar Filato Allah Ya ba mu wata dama a wannan lokaci da muka sam daya daga cikinmu a matsayin dan takarar Gwamnan jihar. Don haka mu taru yi wa Allah godiya kuma mu ci gaba da yin addu’o’in Allah Ya kara ba mu zaman lafiya da kwanciyar hankali a jihar da Najeriya baki daya.