Ban yanke shawarar neman shugabancin kasa ba-Atiku Abubakar
Tsohon Mataimakin Shugaban Kasa Atiku Abubakar ya ce bai riga ya yanke shawarar tsayawa takarar shugabancin Najeriya ba. Idan ba a manta ba, Atiku Abubakar dai ya koma jam’iyyar PDP a kwanakin baya. Inda komawarsa ke da wuya, wasu suke ganin ya koma ne domin ya samu damar yin takarar shugabancin kasa. A wata hira […]

Tsohon Mataimakin Shugaban Kasa Atiku Abubakar ya ce bai riga ya yanke shawarar tsayawa takarar shugabancin Najeriya ba.
Idan ba a manta ba, Atiku Abubakar dai ya koma jam’iyyar PDP a kwanakin baya. Inda komawarsa ke da wuya, wasu suke ganin ya koma ne domin ya samu damar yin takarar shugabancin kasa.
A wata hira da Muryar Amurka, Atiku ya ce idan ya yanke shawarar tsayawa takarar, zai sanar da ‘yan Najeriya.
“Yanzu ban riga na yanke shawarar tsayawa takara ba. Idan na yanke shawarar, zan sanar da duniya,” in ji Atiku.