‘Ban yanke shawarar sake tsayawa takarar Gwamna ba’
Ministar Harkokin Mata, Hajiya Jummai Alhassan, ta bayyana cewa rashin nasarar da APC ta yi a zaben cike gurbi a mazabar dan majalisar jiha na Ardo- Kola ya faru ne bisa dalilai masu yawa. Ta shaida wa wakilin jaridar Aminiya cewa wasu daga cikin magoya bayan APC a jihar ta Taraba sun ki fitowa a […]

Ministar Harkokin Mata, Hajiya Jummai Alhassan, ta bayyana cewa rashin nasarar da APC ta yi a zaben cike gurbi a mazabar dan majalisar jiha na Ardo- Kola ya faru ne bisa dalilai masu yawa.
Ta shaida wa wakilin jaridar Aminiya cewa wasu daga cikin magoya bayan APC a jihar ta Taraba sun ki fitowa a ranar zaben wai don ba su gani a kasa ba, dangane da zaben APC a 2015 da suka yi. Ta kara da cewa wasu kuma sun nemi a ba su kudi kafin su yarda su zabi jam’iyyar, sannan kuma wasu suka ki yarda su bar matansu zuwa wajen zabe.
Hajiya Jummai Alhassan ta ce zaben na cike gurbi wanda aka gudanar a ranar Asabar da ta wuce ya kasance zabe mai kyau wanda ba a yi magudi mai yawan gaske ba. Sannan ta yi zargin cewa a mazabar Jiru kawai ne aka yi wa PDP aringizon kuri’u 300. Ta ce jiga-jigan ‘yan APC sun sa ido matuka wanda haka din shi yasa ba a sami damar aikata magudin zabe kamar yadda aka saba a zabukan baya ba.
“Domin ratar da PDP ta bai wa APC a zaben ba mai yawa ba ne, domin da kuri’u 300 ne kacal. Ba daidai ba ne jama’a su ce dole sai an ba su kudi kafin su jefa kuria, ta ce wannan koma baya ne ga cigaban dimokuradiyya a kasar nan.”
Sannan sai ta nuna takaici bisa yadda aka sabawa magoya bayan jami’yyun siyasa da ba su kudi kafin su jefa kuri’a a ranar zabe wanda hakan ne ya haifar da matsalar rashin shuganci nagari a kasar nan. “Dole ne jama’a su tashi su kwaci ‘yancinsu ta hanyar zaben wadanda zasu samar masu da ayyukan cigaba, ba kawai zaben wadanda za su ba su kudi su zabe su ba.”
Dangane da labaran da ake yadawa cewa ta nuna burinta na sake tsayawa takarar kujerar gwamnan Jihar Taraba, ministar ta ce ba gaskiya ba ne, ta ba furta cewa ta yanke shawarar tsayawa zaben gwamna a shekarar 2019 ba. Tana mai cewa akwai sauran lokaci kuma in lokacin ya yi za ta sanar da al’umma matsayinta.