Ban yi batanci ga dan Fodiyo ba – Sheikh dahiru Bauchi

Fitaccen Malamin Musuluncin nan Sheikh dahiru Usman Bauchi ya karyata zargin da wasu ’yan darikar kadiriya a Jihar Sakkwato suka yi masa cewa ya yi batanci ga Mujaddadi Sheikh Usman dan Fodiyo. Sheikh dahiru Bauchi wanda ya zanta da wakilinmu a Kaduna domin mayar da martani kan zargin matasan kadiriyyar, ya nemi wadanda suke zarginsa […]

Ban yi batanci ga dan Fodiyo ba – Sheikh dahiru Bauchi
Ban yi batanci ga dan Fodiyo ba – Sheikh dahiru Bauchi

Fitaccen Malamin Musuluncin nan Sheikh dahiru Usman Bauchi ya karyata zargin da wasu ’yan darikar kadiriya a Jihar Sakkwato suka yi masa cewa ya yi batanci ga Mujaddadi Sheikh Usman dan Fodiyo.
Sheikh dahiru Bauchi wanda ya zanta da wakilinmu a Kaduna domin mayar da martani kan zargin matasan kadiriyyar, ya nemi wadanda suke zarginsa su fito su fadi abin da ya ce da har suke ganin batanci ne ga dan Fodiyo.
A cewarsa, idan ba su fito fili sun fadi abin da suke zarginsa da shi ba, zai yi kararsu a kotu.
“Na ga wata magana da ta fito a ranar Juma’a 17 ga Yuli a jaridar Aminiya wadda ban ji dadin maganar ba, domin wasu ’yan kadiriyya ne suka ce wai na fadi wata magana da ba ta dace ba game da dan Fodiyo amma kuma ba su fadi maganar da na yi ba. Ni ko ban san na taba fadar wata magana ta batanci ga dan Fodiyo ba. Shehu dan Fodiyo abin girmamawa ne a wajena ba ma shi ba har jikokinsa ina girmamasu banlantana shi da kansa. Wannan bata suna ne saboda haka su fito a jaridar su ba da hakuri in ba haka ba zan iya kai su kotu domin sun bata min suna.”
Ya kara da cewa “Rabona da Sakkwato na dade, wannan bata suna ne kawai da neman tada rigima. Wannan shirri ne kawai wani daga cikinsu ya fadi. In ba haka ba ai sai ya fadi abin da na fada kuma a ina na fada. Ina gargadi da a janye wannan karya da aka yi kuma a ba ni hakuri. Shehu dan Fodiyo abin girmamawa ne a wurina ba abin batawa ba ne. Kowane waliyi ina girmama shi ballantana dan Fodiyo da ke dan kasarmu kuma wanda ya jaddada addini a kasar nan. Na yi Allah wadai da wannan ashararanci da aka yi min.”