Ban yi murabus ba – Aliyu Gusau

Ministan Tsaro Janar Aliyu Gusau ya musanta rahotannin da suka ce ya yi murabus daga mukaminsa a shekaranjiya Laraba a wani al’amari da ya jife damuwa a zukatan jama’a a daidai lokacin da gwamnati ke kokarin magance zubar da jinin da kungiyar Boko Haram ke yi.Janar Gusau ya fadi haka ne a sakon tes da […]

Ban yi murabus ba – Aliyu Gusau

Ministan Tsaro Janar Aliyu Gusau ya musanta rahotannin da suka ce ya yi murabus daga mukaminsa a shekaranjiya Laraba a wani al’amari da ya jife damuwa a zukatan jama’a a daidai lokacin da gwamnati ke kokarin magance zubar da jinin da kungiyar Boko Haram ke yi.
Janar Gusau ya fadi haka ne a sakon tes da ya aike wa jaridar intanet ta Premium Times wadda ta bukaci jin ta bakinsa kan ko ya yi murabus.
Amsar da ya bayar ta zo ne a daidai lokacin da gwamnati ke kokarin musanta jita-jitar murabus din Ministan wanda aka nada a makon jiya, bisa zargin ya samu sabani da kwamandojin sojan kasar nan.
Da farko Kakakin Shugaba Jonathan Dokta Reuben Abati ya ce rahotannin Ministan ya sauka ba gaskiya ba ne.
Ya ce rashin zuwa Gusau wurin taron mako-mako na Majalisar Zartarwa – wanda shi ne dalilin da ake cewa ya yi murabus – ya faru ne saboda rashin lafiya. “Yana   fama da mura ne,” inji Abati.
Rahoton murabus din Janar Gusau ya watsu kamar wutar daji a shekarajiya Laraba bayan da kafar labarai ta Sahara Reporters ta ruwaito wata majiya da ba ta ambata ba cewa takaddama tsakanin Gusau da Babban Hafsan Tsaro Iya Mashal Aled Badeh ce ta jawo murabus din.
Rahoton ya ce Janar Gusau ya mika takardar murabus saboda rashin biyayya daga manyan jami’an soja.
Rahoton ya ce, Iya Mashal Badeh ya tozarta Janar Gusau da Minista a Ma’aikara Tsaro Musiliu Obanikoro bayan sun nuna rashin jin dadinsu kan gazawarsa na shirya taro tsakanin ministocin da manyan hafsoshin sojan kasa da na ruwa da na sama.
Rahoton ya ce Janar Gusau ya yi ta kokarin ganawa da manyan hafsoshin tun bayan rantsar da shi a makon jiya amma ana dagewa, inda a karshe Badeh ya halarci zaman shi kadai.
Kuma da Janar Gusau ya nuna yana bukatar ganawa ne da manyan hafsoshin gaba daya, sai Badeh ya ce sojojin ba za su amince farar hula su rika ba su umarni ba.
Premium Times ta ce wata babbar majiyar tsaro ta tabbatar da cewa an samu takaddamar, sai dai wadanda suka fallasa labarin ga manema labarai sun dan kara gishiri.
Janar Gusau, wanda kwarraren tsohon sojan ne da ake girmamawa ana ganin Shugaba Jonathan ya jawo shi cikin gwamnatinsa ne don dakile ayyukan kungiyar Boko Haram wadda ta jawo mutuwar dimbin jama’a ciki har da yara ’yan makaranta.