Ban yi nadamar komawa PDP ba – Bafarawa

Tsohon Gwamnan Jihar Sakkwato Alhaji Attahiru dalhatu Bafarawa ya ce bai yi nadamar komawa Jam’iyyar PDP ba, inda ya ce komawarsa ta jawo wa al’ummar Jihar Sakkwato alherai ciki har da zuwan da Shugaban kasa ya yi ya ba ’yan kasuwar kara tallafin gobara ‘kan haka ban yi nadamar shiga Jam’iyyar PDP ba,’ inji shi.Tsohon […]

Ban yi nadamar komawa PDP ba – Bafarawa

Tsohon Gwamnan Jihar Sakkwato Alhaji Attahiru dalhatu Bafarawa ya ce bai yi nadamar komawa Jam’iyyar PDP ba, inda ya ce komawarsa ta jawo wa al’ummar Jihar Sakkwato alherai ciki har da zuwan da Shugaban kasa ya yi ya ba ’yan kasuwar kara tallafin gobara ‘kan haka ban yi nadamar shiga Jam’iyyar PDP ba,’ inji shi.
Tsohon Gwamnan ya bayyana haka ne a ranar Lahadin da ta gabata a gidansa lokacin da daliban Jami’ar Usman dan Fodiyo kusan 200 suka kai masa ziyarar godiya kan kudin makaranta da ya biya wa mutum 153.
Ya ce ya shiga PDP ne saboda rokon da mutanensa suka yi ba don yana bukatar shiga ba, “Na shiga jam’iyyar ne don magoya bayana na bukatar haka, ni a yanzu bi nake gare su kawai don in taimaka musu a kawo wa Jihar Sakkwato canji mai amfani da alfanu a shekarar 2015, ni ban karbi ko sisi ba don shiga wannan jam’iyya ba, hukuncin magoya bayana ne na bi,” inji tsohon Gwamna.
Alhaji Bafarawa ya shaida wa daliban wadanda suka fito gidajen talakawa cewa, “Yau ba ranar murna ce ba, rana ce ta bakin ciki, wadannan matasa da suka samu gurabun karatu a jami’a iyayensu ba su da halin biya musu kudin, kuma gwamnati ta kasa biya musu, in ka dubi kudin ba masu yawa ba ne in ka yi la’akari da rayuwar yaran ko a cikin aljihun Gwamna yana iya biyansu in akwai son ci gaban yaran a zuciyarsa.”
Ya ce a shekara takwas da ya yi a kujerar Gwamna tun daga firamare har zuwa jami’a ba dan asalin jihar da ke biyan kudin makaranta. Don haka ya yi kira ga Gwamna mai ci ya ceci rayuwar ’ya’yan jihar daga rushewa, “kuma na san zai ji don ni tsohon mai gidansa ne, in ma haka ba ta samu ba gwamnatin tasu ta zo karshe kuma da yardar Allah in PDP ta kafa Gwamna a Sakkwato ba wani yaro da zai sake biyan kudin makaranta’ inji Bafarawa.
Abdullahi Bashar wanda ya yi magana a madadin daliban, ya ce “Muna gode wa Garkuwa don ka yi mana taimako a lokacin da muke bukata kuma ba za mu ba ka kunya ba, za mu yi tsayin daka don ganin mun samu nasarar karatunmu.”