Ban yi niyyar kashe mijina da reza ba – Amaryar da ta yanki mijinta
Wata amarya da ta yanki mijinta da reza a goshi a ranar Juma’ar da ta gabata bayan daura aurensu da mako uku ta ce ba ta yi hakan da niyyar kashe shi ba. A ranar Juma’ar da ta gabata da dare ne amaryar mai suna Shafa Muhammad ta yanki angonta mai suna Umar Shehu wanda […]

Wata amarya da ta yanki mijinta da reza a goshi a ranar Juma’ar da ta gabata bayan daura aurensu da mako uku ta ce ba ta yi hakan da niyyar kashe shi ba.
A ranar Juma’ar da ta gabata da dare ne amaryar mai suna Shafa Muhammad ta yanki angonta mai suna Umar Shehu wanda ya kai aka yi masa dinki sau biyu a Asibitin Koyarwa ta Usman dan Fodiyo da ke Sakkwato.
Ma’auratan suna zaune ne a Unguwar Arkillar Liman da ke karamar Hukumar Wammako a Jihar Sakkwato kafin faruwar lamarin.
Amarya Shafa Muhammad mai shekara 20 a zantawarta da Aminiya a ofishin ’yan sanda na Arkilla inda ake tsare da ita ta bayyana auren da aka yi mata da cewa na tilas ne ba ta son mijin. Kuma tun kafin auren ta rubuta masa wasika cewa ita ba ta son sa kuma ta gaya masa ya bar zancen aurenta kada su aikata wani abu da zai sa mu yi da- na- sani amma bai ji ba.
Shafa ta ce “A ranar Juma’ar da ta wuce mun samu matsala da mijina mun yi hatsaniya iyayenmu suka yi mana sulhu. Da ya fita gida bai dawo ba har sai da na yi barci. Ina cikin barci ne na ji shi ya haye min a kokarin kwatar kaina ne akwai reza kusa da ni na dauko na yanke shi a kai sau daya. Kuma na yanke shi da rezar ce don kare kaina ba domin in kashe shi ba.”
Ta ce bayan kwana uku na abincin amarci ta shafe kwana bakwai ba ta dora abinci ba “Ba ya ba ni kulawa abinci wani lokaci yayata da wani kanena ne da ke zuwa wurina ke ba ni abinci, sai daga baya iyayena suka sani ba ya ba ni abinci. Kuma kafin aurenmu ya zo wurina na dauki wasika na bai wa wani yaro ya ba shi, bayan ya duba ne ya dawo wurina nake gaya masa duk abin da ya gani a cikin takardar haka ne, ba na sonsa ya bar ni ya tafi ya nemi wata. Tun lokacin da muka yi haka da shi ban sake wata maganar kirki da shi ba. Har ya kawo kaya gidanmu ya san ba na son sa amma ya tsaya kai-da-fata sai ya aure ni, duk da na fada masa ya bari kada mu yi aikin da-na-sani kan zamantakewar. Amma yanzu na yi nadamar abin da na aikata masa don ban zaci yankan zai taba shi haka ba,” inji Shafa Muhammad.
Da wakilinmu ya tambaye ta ko iyayenta sun san ba ta son sa, sai ta ce sun ce ba su san ba ta son sa ba. Sai ta yi kira ga iyaye su daina yi wa mata auren dole su bar su da wadanda suke so su aura.
Ango Umar Shehu wanda aka fi sani da Sanda da ke sayar da Shayi a Unguwar ta Arkilla wanda ya ketare rijiya ya ce, “Da misalin karfe 1:00 na dare na dawo gida daga wurin sana’ata sai na samu Shafa zaune a saman kujera a tsakiyar gida daga nan na fahimci akwai matsala. Ban ce komai ba kawai na ba ta shayinta kamar yadda ta bukata, saboda a lokacin da iyayenta suka yi mana sulhu da zan fita ta ce in zo mata da Shayi kada in zo mata da Indomie ko kwai. Da na ba ta zan wuce ta kira ni Umaru na amsa mata ta ce min don Allah ka sake ni, ta yi tsaye gabana ta matsa min, sai na ce mata yaya za ki hada ni da Allah in saba maSa? In kina son in yi miki yadda kika zaba to ki bari gobe a kira mahaifanki ki maimaita kalaminki zan aikata yadda kika zaba. Ta ce ita ba za ta yi haka ba.”
Umar Sanda mai shekaru 25 ya shaida wa Aminiya cewa “Mun dade muna wannan dambarwar a daren, sai na ce ta je waje ta samo takarda da biro in sake ta, nan ta ce ba kowa a waje in dauko tawa in rubuta mata, na ki yin haka, ta rika zagina ashe tana rike da reza mai kaifi sosai, kawai sai na ji ta yanke ni da ita a goshi, nan take na fita waje ina neman taimakon mutane aka zo aka kai ni asibiti aka kwantar da ni aka yi min dinki biyu a goshin ita kuma ’yan sanda suka kama ta.”
Ya musanta da’awar matar cewa ya san ba ta sonsa da aure, ya ce “In ba ta sona me ya sa ta yi fati a lokacin aurenta duk da an hana yi amma saboda farin ciki ta yi. In ta ce ba na ba ta abinci yau mako uku da aurenmu garar da aka kawo mana ba ta kare ba balle ta ce ban sawo ba. Abin da ya kawo haka a ganina shawarar kawaye ce ko samarinta in tana da su a waje. Ni da ita ’yan uwan juna ne kaddara ce tun da muka yi aure na daina yin dare a waje sai na rika barin wani yaro a teburina abin da Allah Ya kawo ne zan rabu da ita bayan kare batun nan ko tana sona ko ba ta so na ai dai an zo karshe.”
Wakilinmu wanda ya tafi gidan su Shafa ya samu bayanin mahaifinta ya dade da rasuwa mahaifiyarta ba ta da lafiya, yayanta Basiru kuma ba ya gida don haka bai samu jin gaskiyar zargin yi wa Shafa auren dole ba.
Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar Sakkwato ASP Ibrahim Abaras ya tabbatar da cewa amaryar tana hannunsu kuma da zarar sun kammala bincike za su kai ta kotu.
Wani malamin addinin Musulunci a birnin Sakkwato, Malam Murtala da’a ya shaida wa Aminiya cewa “Rashin tarbiyya daga mahaifa da rashin ilimi kan zamantakewar aure an dauki aure al’ada bayan makaranta ce mai zaman kanta da karancin adalci da ake samu wajen maza da mummunan kishi daga bangaren mata na daga cikin dalilan da suke kawo mata su rika daukar makami suna kokarin hallaka mazansu.
Malamin ya ce ko al’ada ta san mata sun fi maza yawa balle addini ya ce a kara aure. Ya ce a Arewa kashi 60 cikin 100 na mutanenta sun tashi a gidansu sun ga ba mahaifiyarsu kadai ce a gidan ba.
Sai ya bukaci a rika aiwatar da hukunci ga masu aikata shaidancin zamani, “Shari’a ba ta aiki, da wata ta ji an kashe wance don ta kashe mijinta da wadansu sun shiga taitayinsu ba da gaske galibin masu shari’a suke yi ba. Samun canjin al’adu da muka yi mun shigo da wasu bakin abubuwa da ba namu ba da shaye-shayen da mata ke yi suna taimakawa ga aukuwar hakan, domin da wuya mace ta sanya wa mijinta makami ba ta sha wani abu ba,” inji Malam da’a.