Ban yi sanadiyyar mutuwar dan Majalisar Tarayya ba – Ma’aikaciyar Banki

Rasuwar dan majalisar wakilai Raphael Oloye Nomiye cikin dare ranar Juma’ar da ta gabata ta haifar da takaddama, inda likitoci suka nuna cewa ya rasu ne bayan ya kammala saduwa da mace, amma budurwarsa ta ce maganin da ya sha, bayan kammala saduwa da ita ne ya yi sanadiyyar rasa ransa.Kakakin rundunar ’yan sanda mai […]

Ban yi sanadiyyar mutuwar dan Majalisar Tarayya ba – Ma’aikaciyar Banki

????????????????????????????????????

Rasuwar dan majalisar wakilai Raphael Oloye Nomiye cikin dare ranar Juma’ar da ta gabata ta haifar da takaddama, inda likitoci suka nuna cewa ya rasu ne bayan ya kammala saduwa da mace, amma budurwarsa ta ce maganin da ya sha, bayan kammala saduwa da ita ne ya yi sanadiyyar rasa ransa.
Kakakin rundunar ’yan sanda mai kula da yankin Abuja, DSP Hyelhira Altine Daniel ta ce har yanzu ’yan sanda na binciken musabbabin rasuwar wannan dan majalisar tarayya mai wakiltar mazabar Ondo da Ilaje da Ese Odo da ke Jihar Ondo mai suna Mista Raphael Oloye Nomiye.
Jami’ar ta ce, duk  da yake dan majalisar ya rasu, jami’an ’yan sanda masu bincike ba su gama bincikensu ba ballantana a gano musabbabin mutuwar tasa.
DSP Daniel ta tabbatar da cewa, Kwamishinan ’yan sanda na yankin Abuja ya umarci ’yan sanda masu binciken manyan laifuka (State CID) da su amshi binciken maganar daga ofishin ’yan sanda na yankin Gwarimpa.  
Ranar Juma’a da asuba ne Mista Raphael ya yanke jiki ya fadi a lokacin da yake kokarin shiga bandaki a gidansa bayan da ya gama saduwa da budurwarsa, wata ma’aikaciyar banki a gidansa da ke Gwarimpa a babban birnin tarayya, Abuja.
Jami’ar bankin, wadda tuni ’yan sanda suka yi awon gaba da ita, ta bayyana wa ’yan sanda cewa bayan da ta sadu da dan majalisar a dakinsa suka share jikinsu, sai dan majalisar ya hadiyi kwayar maganin panadol da ruwan roba.
Ta ce bayan da ya sha maganin, sai ya daura tawul ya kama hanyar shiga bandaki sai ya fadi ya fara aman jini. Ta ce ba ta yi wata-wata ba sai ta gangaro daga gidan saman ta samu ’yan sandan da ke gadin gidan a kasa ta yi musu bayanin halin da maigidan yake ciki.
Jami’ar bankin ta bayyana wa ’yan sanda cewa masu gadin gidan ne suka taimaka mata aka dauke shi a motarsa zuwa babban asibitin kasa (National Hospital) da ke Abuja a inda aka tabbatar da rasuwarsa.
’Yan sanda ba su yi wata-wata ba sai suka cafke jami’ar bankin suka rufe ta a ofishinsu na Gwarimpa tun ranar Asabar da asuba, sannan aka kai ta ofishin CID da ke Garki.
Sai dai wata majiya ta bayyana cewa an bayar da belinta tun ranar Litinin da ta gabata. Abokan aikinta da ke bankin Zenith na reshen majalisar tarayya sun ce ta koma bakin aiki.
 Shi dai wannan dan majalisa wanda ya fito daga Jihar Ondo ana zargin ya rasu ne bayan ya kammala saduwa da ma’aikaciyar banki a gidansa da ke rukunin gidaje na Gwarinpa a Abuja.
Rahael Oloye Nomiye, dan shekara 50, yana wakiltar mazabar Ondo da Ilaje da Ese Odo na jihar Ondo a Majalisar Tarayya a karkashin inuwar jam’iyyar Labour, an ce ya gamu da ajalinsa ne bayan daukar lokaci mai tsawo da ya yi yana saduwa da budurwar tasa mai suna Ajoke Ohaneme, wadda ke aiki a wani banki a Abuja.  
A yayin da Aminiya ta ziyarci gidan marigayin, makwabtansa sun bayyana wa wakilinmu cewa budurwar tasa, wadda ita ce ke kula da asusun ajiyarsa na banki,ita ce ta sauko a guje daga saman bene ta bayyana wa ‘yan sandan da ke gadin gidan cewa, “maigida ya fadi kuma yana aman jini.’’
Majiyar tamu ta nuna cewa, lokacin da ‘yan sandan suka isa cikin dakin nasa da ke saman bene sun tarar da marigayin kwance a kasa daure da tawul, jini na fitowa daga bakinsa. Daga nan sai suka kwashe shi a cikin motarsa kirar Camry 2012 mai lamba 1433 Rep, zuwa wani asibitin kudi da ke 3rd Abenue a cikin rukunin gidajen na Gwarinpa. Sai dai kuma likitocin asibitin sun ki karbarsa, domin sun ce al’amarin ya fi karfinsu, saboda haka sai suka garzaya da shi babban asibitin kasa da ke Abuja, inda aka tabbatar da cewa ya riga ya rasu.
A lokacin da ‘yan sandan ofishin yanki na Gwarinpa suka kama Ajoke ta musanta cewa marigayin ya yi lalata da ita, amma da likitoci a babban asibitin kasa suka matso maniyyin da ya rage a cikin azzakarin marigayin suka yi gwaji suka tabbatar cewa ya sadu da mace gab da rasuwarsa, sai Ajoke ta amince cewa lallai marigayin ya sadu da ita, har ma ta taimaka masa wajen share azzakarinsa da takardar share ba-haya, lokacin da danmajalisar yake kokarin shiga bandaki domin ya yi wanka ne sai ya fadi, jini ya rika fitowa ta bakinsa.
‘Yan sandan da suka yi bincike a gidan marigayin sun gano takardar share ba-hayan da Ajoke da marigayi Raphael suka yi amfani da ita wajen share azzakarin nasa da suturar da ya sanya kafin ya sadu da ita.
Da Aminiya ta je gidan da Ajoke take a rukunin gidaje na Kado a Abuja, abokan aikinta guda biyu wadanda suka bukaci a sakaya sunansu, sun bayyana wa wakilanmu cewa, Ajoke da Raphael sun dade suna soyayya a tsakaninsu, kodayake sun ce ba su san suna lalata da junansu ba, kuma ba su da labarin akwai wata jikakka a tsakanin masoyan biyu.
A binciken da Aminiya ta gudanar ta gano cewa, duk da cewa marigayi danmajalisan yana da aure, amma ba ya tare da matarsa da ‘ya’yansa a Abuja.
Kawun marigayin mai suna Cif Charles Temitan, ya bayyana cewa, rasuwar Raphael ta girgiza shi, “domin na rabu da shi da misalin karfe uku na ranar Juma’a lafiya lau, ban san cewa ashe haduwarmu ta karshe da shi ke nan ba, rasuwarsa babban rashi ne a gare mu. Makonni biyu da suka gabata ya yi ruwa, ya yi tsaki a wajen jana’izar surukinsa a Sabome da ke karamar Hukumar Ese-Odo ta jihar Ondo.’’
Mista Jackson Nomiye, wanda kanen marigayin ne, ya ce gwamnatin Jihar Ondo da wakilan majalisar wakilai da iyalan marigayin sun amince a gudanar da bikin jana’izarsa a tsakanin ranakun 6 da 7 ga watan Disamban nan.
Ya karyata zargin da ake yi cewa dan uwansa ya rasu ne sanadiyyar saduwa da budurwar, yana mai nuni da cewa tuntuni dan uwan nasa ba shi da koshin lafiya.
An haifi marigayi danmajalisar wakilai Raphael ne a ranar 2 gawatan Yunin shekarar 1963, ya samu digiri a fannin mulki daga jami’ar Benin ta jihar Edo a shekarar 2006.
An zabi marigayi Raphael a matsayin danmajalisar wakilai ne a watan Afirilun shekarar 2011, a karkashin inuwar jam’iyyar LP.
Raphael wanda jinin sarauta ne, mahaifinsa shi ne Mista Jeremiah Sego Nomiye da ke Molutehin a karamar Hukumar Ilaje ta Jihar Ondo.