Ban yi wa na kasa da ni adalci ba idan na maimaita kujerar minista — El-Rufai

Na horar da mutane da dama wadanda sun cancanci su gaje ni a fannoni daban-daban.

Ban yi wa na kasa da ni adalci ba idan na maimaita kujerar minista — El-Rufai

Tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Nasiru El-Rufai, ya bayyana cewa babu adalci ya maimaita kujerar minista a yayin da shekarunsa suka ja.

El-Rufai ya yi wannan furuci ne a wani tsohon bidiyo da aka nada yana tattaunawa da wasu mutane da ba a iya tantance su ba.

Ana iya tuna cewa, El-Rufai ya rike mukamin Ministan Abuja daga shekarar 2003 zuwa 2007 a zamanin mulkin tsohon Shugaban Kasa Cif Olusegun Obasanjo.

Sai dai a halin yanzu, sunan tsohon gwamnan ya sake bayyana a cikin jerin sunayen ministocin da Shugaba Bola Tinubu ya mika wa Majalisar Tarayya domin tantancewa.

A wancan tsohon bidiyo da a yanzu ya sake karade dandalan sada zumunta, an nadi El-Rufai yana bugun kirjin cewa ba zai yiwu ya sake rike mukamin minista ba, domin kuwa hakan ya nuna bai yi nasara a rayuwa ba ke nan.

A cikin bidiyon, El-Rufai ya ce, “ta ya za a yi ka rike mukamin minista kana dan shekara 43 sannan kuma bayan shekara 20 ka sake maimaita wannan mukami bayan ka kai shekaru 63 ke nan a doron kasa?

“Ina ’ya’yanka ko ’yan uwanka na kasa da kai, shi su ba za su zama ministoci ba ke nan?

“Shin ko an yi wannan mukami kadai don saboda kai? Wannan ba abu ba ne da ya kamata.

“Ina yi wa Allah godiya da ya ba ni sa’ar zama Ministan Abuja ina da shekaru 43 a ban kasa.

“A badi fa zan cika shekara 63. Sannan kuma na sake maimaita kujerar minista.

“Shin babu wanda ya cancanci kujerar a cikin ’ya’yana ko ’yan uwana na kasa da ni?

“Idan har haka ta kasance ya nuna ke nan na gaza kuma ban yi nasara ba wajen dora su a kan turbar da ta dace a fagen horar da su.

“Na horar da mutane da dama wadanda sun cancanci sun gaje nina fannoni da dama.”

Gwamnatin Kano na shirin tara harajin 80bn a 2025

Kirsimeti: Zulum ya ɗauki nauyin jigilar fasinjoji 710 zuwa garuruwansu

Ɗan shekara 60 ya rasu a hatsarin kwalekwale a Sakkwato

Yadda gobara ta ƙone kasuwar babura a Zamfara