Bana azumi 30 za a yi a Najeriya – Sarkin Musulmi
Kamitin duban wata na fadar Sarkin Musulmi ya tabbatar da cewa ba’a samu ganin jinjirin watan Shawwwal ba Najeriya a ranar Juma’a. A cikin wata sanarwa da kwamitin ya wallafa dazun nan a shafinsa na Twitter, ya tabbatar cewa rashin ganin jinjirin watan ya sa za a cike azumin bana zuwa 30. Hakan dai ke […]
Kamitin duban wata na fadar Sarkin Musulmi ya tabbatar da cewa ba’a samu ganin jinjirin watan Shawwwal ba Najeriya a ranar Juma’a.
A cikin wata sanarwa da kwamitin ya wallafa dazun nan a shafinsa na Twitter, ya tabbatar cewa rashin ganin jinjirin watan ya sa za a cike azumin bana zuwa 30.
Hakan dai ke nan ya nuna cewa sai ranar Lahadi za’a 24 ga watan Mayun da muke ciki za a yi Sallar Idin.
Hakazalika, a wata takardar da wazirin Sakkwato kuma shugaban kwamitin ganin wata a majalisar Sarkin Musulmi ya sanyawa hannu aka rabawa manema labarai ya ce Sarkin Musulmi Alhaji Sa’ad Abubakar ya aminta da cewa ranar Lahadi ce 1 ga watan Shawwal 1441 ranar sallah kenan.
Sarkin Musulmi ya yi kira ga mutanen kasa su cigaba da addu’ur zaman lafiya da cigaban al’umma.