Bana farashin doya ya fadi – Basiru Maidoya
Wani mai sayar da doya a Kasuwar ’Yan doya da ke Birnin Kebbi a Jihar Kebbi, Alhaji Basiru Maidoya ya ce bana farashin doya ya fadi, sakamakon yadda manoma suka noma ta da yawa da kuma yadda Allah Ya kawo albarkarta. Alhaji Basiru Maidoya ya bayyana haka ne a lokacin da yake zantawa da Aminiya, […]
Wani mai sayar da doya a Kasuwar ’Yan doya da ke Birnin Kebbi a Jihar Kebbi, Alhaji Basiru Maidoya ya ce bana farashin doya ya fadi, sakamakon yadda manoma suka noma ta da yawa da kuma yadda Allah Ya kawo albarkarta. Alhaji Basiru Maidoya ya bayyana haka ne a lokacin da yake zantawa da Aminiya, inda ya ce “Harkokin kasuwacin doya a bana sun yi daban da bara. Domin a bana an yi noman doya da yawa kuma Allah Ya kawo albarkarta don haka a bana doya ta yi sauki sosai domin doyar da ake sayarwa a bara kan Naira 300 a bana ana sayar da ita kan Naira 200. Doyar da ake sayarwa Naira 400 a bara, a bana ana sayar da ita Naira 300. A bana mun fi samun ciniki saboda faduwar farashin doyar. Domin a bara mutane da dama doyar ta gagare su saboda tsadarta.”
Alhaji Basiru Maidoya ya ce a kasuwar doya ta garin Birnin Kebbi, suna zuwa su sayo doyar da suke sayarwa a garuruwan Odoba da Paiko da Lambata da Zungeru da kuma Mariga duk a Jihar Neja.
Ya ce ya samu ci gaba sosai a wannan harkar ta kasuwancin sayar da doya, domin ya yi gida ya yi abin hawa kuma yana samun abin da yake ciyar da iyalansa da biya wa ’ya’yansa kudin makaranta, kuma yana taimaka wa na kasa da shi. Daga nan ya yi kira ga masu kasuwancin doya, su rike gaskiya da amana a wajen gudanar da harkokinsu.
Ya kuma yi kira ga gwamnatocin Arewa su fito da hanyoyin tallafa wa kananan ’yan kasuwa a kasar nan, saboda sun fi ma’aikata yawa. “Don haka ya zama wajibi a taimaka musu domin inganta kasuwanci a Arewa,” inji shi.
Ya ce dole Gwamnatin Tarayya da na jihohi da kuma ’yan majalisa su bullo da hanyoyin tallafa musu kamar yadda suka tallafa wa manomana kasar nan.
Alhaji Basiru Maidoya ya kara da cewa akasarin kungiyoyin kananan ’yan kasuwa a Arewancin kasar nan ba su samun tallafi daga shugabanninsu domin inganta kasuwancinsu, su tuna nan da ’yan watanni kadan zabe na zuwa duk ’yan kasuwa na nan rike da katin zabensu.