Bana farashin doya ya fadi – Umaru Maidoya

Wani mai sayar da doya a kasuwar ‘yan doya dake garin Jos, babban birnin Jihar Filato, Alhaji Umaru Maidoya, ya bayyana cewa bana farashin doya ya fadi, sakamakon yadda manoma suka noma ta da yawa da kuma yadda Allah Ya kawo albarkarta. Alhaji Umaru Maidoya ya bayyana haka ne a lokacin da yake zantawa da […]

Bana farashin doya ya fadi – Umaru Maidoya

Wani mai sayar da doya a kasuwar ‘yan doya dake garin Jos, babban birnin Jihar Filato, Alhaji Umaru Maidoya, ya bayyana cewa bana farashin doya ya fadi, sakamakon yadda manoma suka noma ta da yawa da kuma yadda Allah Ya kawo albarkarta. Alhaji Umaru Maidoya ya bayyana haka ne a lokacin da yake zantawa da jaridar Aminiya.

Ya ce gaskiya harkokin kasuwancin doya a bana sun yi daban da bara. Domin a bana an yi noman doya da yawa kuma Allah Ya kawo albarkata. “Don haka a bana doya ta yi sauki sosai da sosai domin doyar da ake sayarwa a bara kan kudi naira 300 a bana suna sayar da ita kan naira 200. Doyar da suke sayarwa naira 400 a bara, a bana suna sayar da ita naira 300. A bana mun fi samun ciniki saboda faduwar farashin doyar. Domin a bara mutane da dama doyar ta gagare su saboda tsadarta”.

Alhaji Umaru Maidoya ya yi bayanin cewa a wannan kasuwar doya ta garin Jos, suna zuwa su sayo doyar da suke sayar wa a garuruwan Yelwan Shendam da Namu da Yamani da Kuka dake nan Jihar Filato. Har’ila yau ya ce suna zuwa Wukari dake jihar Taraba da Lambata dake Jihar Neja suna sayo wannan doya.

Ya ce ya sami cigaba sosai a wannan harka ta kasuwancin sayar da doya, domin ya yi gida ya je aikih hajji kuma yana samun abin da yake ciyar da iyalansa da biyawa ‘yayansa kudin makaranta. Daga nan ya yi kira ga masu wannan kasuwanci na sayar da doya, su rike gaskiya da amana a wajen gudanar da harkokin wannan kasuwanci.

Majalisa ta buƙaci sojoji su kawo ƙarshen Lakurawa

Ɗan Aljeriya ya shiga hannu kan safarar makamai a Zamfara

’Yan bindiga sun kashe ’yan banga sun sace mai unguwa a Kaduna

A wata 19 Tinubu ya ciyo bashin tiriliyan 50