Raguna sun yi tsadar da ba su taba yi ba a Sakkwato
Raguna sun yi tsadar da ba su taba yi ba a Sakkwato a yayin da farashin dabbobi ya karu da kashi 70 a Bauchi
Yayin da Babbar Sallah ke kara karatowa, magidanta da dama sun fara ziyartar kasuwannin sayar dabbobi don sayen raguna da sauran dabbobin da za su yi layya da su da kuma wadanda za a yanka don yin abincin bikin salllar.
Sai dai a bana, tashin gwauron zabon da farashin raguna ya yi, ya sa magidanta da dama masu niyyar yin layya cikin shakkun ko za su iya sayen ragon layya? Aminiya ta kai ziyara a wasu daga cikin kasuwannin dabbobi na sassa daban-daban na fadin kasar nan, inda ta zanta da masu saye da kuma masu sayar da dabbobin don jin yanayin yadda kasuwar dabbobi ke tafiya.
A Legas
A Jihar Legas, kasuwannin dabobbi manya da kanana sun cika sun tunbatsa, sai dai dabobbin sun yi tsada fiye da kima idan an kwatanta su da shekarun baya. Masu sayar da dabobbin na alakanta tsadar man fetur da ya janyo tsadar rayuwa baki daya.
Bayan manyan kasuwanin raguna irin su Alaba Rago da kasuwar rago ta Mangwaro a Agege da ta Abbatuwar Legas, a bana an sami karuwar wuraren sayar da ragon layya a cikin unguwani a Agege da sauransu. Kuma a cewar wani mazaunin garin Agege, Muhammed Kabir, bana an sami mutane da dama mazauna Legas da suka shiga harkar sayar da dabobbin a maimakon a baya da ake dogaro da ‘yan cirani da ke kawo dabobbin layya daga Arewa.

“Idan ka lura a bana tun kafin fataken dabobbin su iso, ‘yan gari da suka shiga harkar sun baza tasu hajar, wadanda su ma sun sayi dabobbin ne suka turke su. Kuma da alamu duk sun ci buri a kansu, amma muna sa ran shigowar bakin fataken raguna daga Arewa. Sannan rashin kudi a hannun jama’a zai iya sauya fasalin farashin ragunan nan gaba,” in ji shi.
Ya kara da cewa, “tunda yake akwai hauhawar farashin man fetur wanda ya janyo tsadar dabobbin, amma idan an sami karacin masaya, dole farashin ya sauka fiye da yadda ake za to,” in ji shi.
Alhaji Abdulhamid Condo da ke zaune a garin Abeokuta, ya shaida wa Aminiya cewa, a bana ya yi tanadin ragunan layya na sayarwa sama da guda 500 wanda ya turke su domin sayarwa a lokacin salla babba.
Ya ce, ya fara sayar da ragunan tun gabanin sallar da kwana 10, kuma ya saukaka farashin domin bai wa jama’a damar sayen dabobbi don yin layya cikin rahusa don samun lada daga Allah.
“Ka ga a nan muna da kananan raguna masu kyau, ‘yan Naira dubu 200 zuwa Naira dubu 250, kana akwai matsakaita ‘yan Naira dubu 300 zuwa Naira dubu 800 sai manyan raguna da farashinsu ke farawa daga Naira miliyan daya zuwa miliyan daya da dari biyar zuwa sama,” in ji shi.

Malam Rabi’u dan Azumi magidanci ne da ke zaune a garin Idiyarba a Legas, ya shaida wa Aminiya cewa, farashin ragon layyar sau tari ya danganta ne da masu sayarwa. Inda wasu ke cin buri sai sun sami riba mai yawa, yayin da wasu ke saukakawa, “wannan ne ya sa mutane ke zagayawa kasuwanni da dama, duk inda ya fi sauki sai su saya,” in ji shi.
Ya kara da cewa, “ka ga ni da na lura da dawainiyar da ke kaina ta iyalina da ‘yan’uwa da abokan arzini, a maimakon in sayi ragon Naira dubu 700 wanda namansa ba zai je mana ko ina ba, sai na sayi dan marakin na Naira dubu 700. Domin a jikinsa sai na fi samun wadataccen nama da zan yi kyauta da sadaka kuma mu ci da iyalina,” in ji shi.
Malam Nuhu Usman da ke sayar da dabbobin a Legas, ya shaida wa Aminiya cewa, suna biyan kudin dakon saniya a manyan motoci daga Arewa zuwa Legas a kan Naira dubu 70 zuwa Naira dubu 100 kan kowace saniya ko sa, yayin da suke biyan Naira dubu 30 ga rago daya.
“Baya ga tsadar abincin dabobbin, wannan na cikin abubuwan da ya janyo tsadar dabobbin, amma muna fatan samun kasuwa musamman ma da yanzu ake gabar siyasa. Muna kyautata zaton ‘yan siyasa za su sayi raguna sosai su raba wa mutanensu,” in ji shi.
A Jihar Ogun ma haka abin yake, inda karamin rago ke farawa daga Naira dubu 200 zuwa dubu 300, yayin da matsakaita ke farawa daga Naira dubu 500 zuwa dubu 800. Sai manyan raguna da ke farawa daga Naira miliyan daya zuwa miliyan biyu.

Farashin dabbobi ya karu da kashi 70 a Bauchi
Yayin da ya rage mako guda a yi Babbar Sallah, farashin raguna ya yi tashin gwauron zabo a sassa daban-daban na Jihar Bauchi
Binciken da wakilin Aminiya ya yi a kasuwannin dabbobi a Jihar Bauchi, ya gano farashin raguna da shanu ya karu da akalla kashi 70 cikin 100.
A kasuwar shanu da ke Bauchi, Abdullahi Sani da Aliyu Sabi’u na daga cikin dillalan dabbobi, sun bayyna cewa, da yawa mutane na zuwa su tambayi farashin raguna, amma su tafi ba tare da sun saya ba. Ko kuma su ce, za su je su yi shawara, lamarin da ya sa kasuwar ta yi nauyi sosai.
Bincike ya nuna cewa, farashin raguna a bana ya haura na bara sosai, lamarin da ya sa mutane da dama ke kokawa kan rashin karfin sayen abin yin layya.
A kasuwar Shanu da ke Bauchi karamin rago da aka sayar tsakanin Naira150,000 a bara, yanzu ya kai tsakanin Naira 185,000 zuwa Naira 200,000, har zuwa Naira 250,000
Matsakaicin rago kuma da aka sayar tsakanin Naira 250,000 a bara, yanzu ya kai tsakanin N300,000 zuwa N450,000. Yayin da manyan raguna suke kaiwa har Naira dubu 500,000 zuwa Naira 800,000 har miliyan daya.
daya daga cikin dillalan dabbobi a kasuwar Wunti da ke Bauchi, Alhaji Abdullaki Yakubu, ya ce, tsadar dabbobin na faruwa ne sanadin tsadar man fetur wanda ya jawo karin kudin mota da kuma tsadar abincin dabbobi.
Ya ce, “za mu je kauye mu sayi dabba amma kudin kawo ta Bauchi ya kai kusan kudin dabbar, ga tsadar abincin dabbobi. Akalla saniya kowace rana za ta ci abincin Naira 2000 zuwa Naira 3000.”
Abdulbaki ya shawarci jama’a, su yi hakuri wanda yake da hali ya yi layya, sannan masu hali su taimaka wa jama’a marasa karfi.
A wasu kasuwanni da ke kauyukan Bauchi, kamar kasuwar Durum da Dass da Nabordo, wasu masu sayen dabbobi suna tafiya ne kai tsaye zuwa rugar Fulani don sayen raguna daga makiyaya saboda saukin farashi idan aka kwatanta da sayen raguna a hannun dillalai a kasuwanni.
Wasu da suka saba yin layya sun ce, bana da kyar za su iya yi, saboda matsin tattalin arzikin da suke ciki. Kodayake wasu sun bayyana fatan cewa, a bana ma za su yi idan an samu an yi albashi kafin sallar.
Bincken da Aminiya ta gabatar, ya nuna farashin shanu ma ya ninka, inda karamar saniya ta kai Naira 450,000, matsakaiciya kuwa ana sayar da ita a kan Naira 750,000. Yayin da farashin manyan shanu yake kamawa daga Naira 1,000,000 zuwa Naira miliyan 3.

Da yake bayanin yadda kasuwa ke basu kashi, Malam Sunusi Mai saniya ya ce, an samu tsadar shanu da raguna ne sakamakon tsadar kudin mota. Bayan tashin farashin man dizel da manyan motocin da ke dakon dabbobin ke amfani da shi.
Ya ce, “mu ma mun san bana abubuwa sun yi wahala, amma duk da haka mutane na zargin mu da tsawwala kudin raguna.
“Ya kamata su fahimci ba laifinmu ba ne, yanzu kusan babu abin da kudinsa bai karu ba a kasar nan.”
Ya ci gaba da cewa, “hatta masu turke dabbobin a gidaje za su gaya muku abincin dabbobi ya yi tsada, don haka hakuri kawai jama’a za su yi,” in ji shi.
Raguna sun yi tsadar da ba su taba yi ba a Sakkwato —Masaya
Binciken Aminiya ya gano cewa, magidanta sun shiga damuwa kwarai da gaske saboda tsadar kayayyaki da dabbobi yayin da Babbar Sallah ta karato musamman ma wadanda suke da niyyar layya.
Wannnan sallar ta zo dana ta salon da magidanta suka koka kan tashin gauron zabo da dabbobi suka yi a kasuwa, abin da ya kai ga dole wasu suka hakura da niyyarsu ta yin layya. Inda da dama suka bayyana cewa, a halin yanzu za su yanka kaji ne madadin rago ko akuya.

Mainasara Muhammad daya daga cikin masu sana’ar sayar da dabbobi a kasuwar Kara, babban wurin sayar da dabbobi a Birnin Sakkwato ya ce, “ wannan shekara dabbobi sun yi kudi da yawa, ragon da zai yi layya zai fara ne daga Naira dubu 200, tunkiya kuwa farashinta ya fara daga Naira 150. Yayin da akuya za ka samu ta Naira dubu 80. Amma in ka yi la’akari da shekara baya ragon Naira 150 babba ne wanda zai yi maka layya sabanin yanzu.”
Kan batun masu sayen dabbobi, Mainasara ya ce, “muna da karancin masu sayen dabbobi a yanzu, mutane sukan zo da sun ji farashin dabba ya yi sama sai su tafi abinsu.
“Amma ba mu damu ba domin a al’adar Sakkwato cinikin dabbobi ya kan kama ne kwana hudu kafin sallah. Haka za ka ga ana ta hada-hada domin shi Basakkwace bai iya zama sai ya sayi abin layya sannan hankalinsa ya kwanta,” a cewar Mainasara.