Bana na ga gawar Fir’auna
Tsakanin 16 ga Fabrairun da ya gabata zuwa 3 ga watan nan na Maris na dan yi bulaguro na kwana 16, zuwa kasashen Saudiyya da Masar. Mun bar Kano a ranar 16 ga Fabrairu zuwa birnin Madina na kasar Saudiyya don aikin Umrah da Allah Ya nufe ni da in sake yi. Mun samu kwana […]
Tsakanin 16 ga Fabrairun da ya gabata zuwa 3 ga watan nan na Maris na dan yi bulaguro na kwana 16, zuwa kasashen Saudiyya da Masar. Mun bar Kano a ranar 16 ga Fabrairu zuwa birnin Madina na kasar Saudiyya don aikin Umrah da Allah Ya nufe ni da in sake yi. Mun samu kwana uku a Madina, kuma kamar yadda addini ya tanada mun ziyarci Raudar Manzon Allah (SAW) da na sahabbansa da kuma Bakiya inda kushewar wasu daga cikin sahabbansa suke da sauran muhimman wuraren tarihi na birnin Madina, kamar yadda Sunnah ta tanada.
Na fahinci cewa ana dan sanyi-sanyi a birnin na Madina kasancewar, manya-manyan na’urorin nan da suke sanyaya Masallacin Manzo dare da rana, sanyin da kana daga nesan kofar shiga masallacin za ka ji tamkar ka doso wani babban gulbi ko tafki da dare kuma a ce a lokacin sanyin hunturu ne. Kodayake ana kunna na’urorin, amma a can kasa-kasa kwarai sosai.
Kasancewar yanzu ba lokacin Aikin Hajji ba ne ko na azumin watan Ramadan, lokata biyu da al’ummar Musulmin duniya suka fi ziyartar kasar Saudiyya, cikin masallacin ba ya da cikowar masu ibada, koda kuwa a lokutan sallolin farilla ne. Hakazalika cikin mintuna biyar sai ka yi ziyara ka fita, wato dai ba cinkoso na irin wadancan lokuta da na ambata.
Mutanen Madina suna nan da karamcinsu na girmama baki, ta yadda a ranakun Litinin da Alhamis wadansu kan kawo shayi da gahawa da gurasa da dabino don masu azumin nafila.
Bayan kwana ukun mun zarce zuwa Jiddah, a wannan karon ta jirgin kasa. Na kuma yi matukar jin dadin tafiyar, kasancewar muna ta hira da ganin garuruwan kan hanya Ni da abokan tafiyar tawa da suka hada da Ambasada Yahaya Kwande da Alhaji Muhammadu Babandede Magajin Rafin Hadeja da Alhaji Dahiru Idi wani dan kasuwa a Kano.
Na yaba matuka da yadda jirgin kasan yake da kyau da kuma tsarin yadda hukumar take tafiyar da shi, wajen tashi da isa a kan lokacin da ta tsara. Amma Ambasada Kwande ya shaida min cewa, ai jirgin kasanmu da yake ziga-zirga a tsakanin Abuja zuwa Kaduna, ya ma fi na Saudiyya din kyawun kira. Gaskiya na yi matukar jin dadi da jin hakan, tare da yin addu’ar Allah Ya ba mu ikon inganta dukkan ayyukanmu.
Mai karatu daga Jiddah muka je Makka don yin Umara da Dawafin Nafila, kai har da Sallar Juma’a. Na fahimci mahukuntar kasar Saudiyya sun dawo kan aikin fadadawa da kawata Harami gadan-gadan, ta yadda daga nan zuwa lokacin Aikin Hajjin bana maniyatan da Allah Ya nufa da zuwa za su ga abin da nake fadi.
A ranar Talata 25 ga Fabrairu mun bar Jiddah zuwa Alkahira babban birnin kasar Masar, a zaman yin hutu na kwana bakwai.
Wannan shi ne karo na uku ina zuwa kasar Masar, wato a shekarar 2018 da 2019 da kuma bana. Kasar ta Masar duk da ta kasance a cikin Nahiyar Afirka ta Arewa, amma ci gabanta ta kowane fanni za ka iya kwatanta shi da na kasashen da suka ci gaba a Nahiyar Turai da na sauran Tekun Fasha, a fannin gine-gine da sufuri da kiwon lafiya da makamantan ayyukan ci gaban kasashen duniya.
Wani babban abu da kasar ta Masar take amfani da shi wajen kawo mata makudan kudaden shiga musamman daga baki ’yan kasashen waje, bayan fannin kiwon lafiya, sai kuma harkokin yawon bude-idanu.
A fannin harkokin yawon bude-idanun a shekarar 2018, na samu halartar gagarumar Dalar nan tare da jagoran tafiyarmu, Alhaji Aminu Dantata da Ambasada Kwande da Magajin Rafin Hadeja Alhaji Muhammadu Babandede da Sakataren Alhaji Aminu Dantata Alhaji Mustapha Abdullahi Junaidu.
A koyaushe a wajen Dalar cike yake da motoci daga kamfanonin tafiye-tafiye da harkokin yawon bude idanu na kasar Masar da suke kawo cincirindon baki ’yan yawan bude-idanu da mutum zai yi tsammanin wata gagarumar kalankuwa ake gudanarwa.
Idan ka shiga cikin harabar Dalar ba abin da za ka gani sai jama’a kowa na yin abin da ya kawo shi, wadansu kan rakuma, wadansu a kan dawakai, wadansu sun ba Dalar baya ana daukarsu hoto bisa yadda suke bukata. Kazalika inda duk kuma ka duba masu saye da sayarwa ne na kayayyakin gargajiya iri-iri na kasar Masar.
Mai karatu kada ka manta cewa fafajiyar Dalar gaba dayanta kasa ce, ma’ana ba gyara ko kwaskwarima da aka yi mata don kawatawa.
A ziyarata ta bana, a ranar Litinin da ta gabata, ni da abokin tafiya Alhaji Dahiru Idi, mun samu halartar katafaren gidan kayayyakin tarihi na kasar Masar da yake cikin babban birnin kasar. Gidan kayan tarihin mai bene hawa daya, a takaice, budadden wuri ne sama da kasa, ta yadda za ka iya kewaye kowane sashe, amma kuma za ku iya bace wa junanku saboda irin yawan mutanen da ke kara-kaina don kashe kwarkwatar idanuwansu.
Ina son mai karatu ya kaddara a zuciyarsa duk wani abu na tarihin kasarsa na amfani don sana’o’i ne, ko al’ada, ko na karatu da rubutu, ko wasu shahararrun mutane da suka yi gwagwarmayar tabbatar da kasar da makamantan kayayyakin tarihin kasa, to akwai su a cikin wannan gidan tarihi, kamar wadansu shahararrun mutanen kasar ta Masar mutun- mutuminsu aka yi.
Duk inda ka yi maganar tarihin kasar Masar, musamman ga Musulmi, ba abin da zai zo maka a zuciya sai tarihin Fira’auna da ya yi zamani da Annabi Musa (AS), amma abin mamaki, kamar yadda na gane wa idanuna, ba kasafai masu ziyarar gidan tarihin suke kara biyan kudi su shiga dakin musamman da ake ajiye da gawar ta Fira’auna da sauran wasu gawarwaki bakwai na sarakunan kasar ba. Kafin a shiga gidan mutum zai biya Fam 200, kwatankwacin Naira dubu 4, 600 yayin da sai kuma mutum ya kara biyan wasu Fam 180, kwankwacin Naira 4,140.
Mu dai mun biya, mun kuma kashe kwarkwatar idanuwanmu wajen ganin gawar Fira’aunan Annabi Musa (AS), wanda aka ce ya shafe shekara 67 yana mulkin Masar.
Duk yadda za ka iya kawo siffarsa a kan fari ne ko baki, dogo ko gajere, mai kiba ne ko ramamme ne, zai yi wahala, kasancewar kwarangwal dinsa duk ta canja bisa ga tsawon lokacin da yake ajiye na sama da shekara dubu 6 da mutuwarsa.
Kamar yadda na saba yin addu’a ga kasar nan a duk lokacin da na ziyarci wata kasa, na ga irin ci gaban da ta samu walau ta fannin tattalin arziki da na zamantakewa da na tsaro da zaman lafiya, a wannan karon ma ina mai addu’a ga Allah (SWT) Ya ba mu ikon yin katafaren gidan adana kayayyakin tarihinmu da ganin ingantuwar wutar lantarkinmu da hanyoyi da dawo da zaman lafiya. Ina kuma addu’ar Allah Ya kara saka wa mai daukar nauyin tafiye-tafiyenmu da mafificin alheri duniya da Lahira. Ya yawaita arzikinsa tare da duba bayansa Ya sa kuma ya cika da imani, ya tashi da imani. Haka sauran masu dawainiya da mu.