Bangaren masaku na bukatar garambawul – Gwamnati
Gwamnatin Tarayya ta ce, kamfanonin masaku na bukatar garambawul cikin gaggawa saboda inganta karin abin da Najeriya ke samarwa a shekara (GDP). A yayin taron kungiyar masu bincike na masaku ta Najeriya (TRAN) na duniya karo na 6, Ministan Kimiyya da Fasaha Dokta Ogbonnaya Onu ya bayyana muhimmancin garambawul ga masakun. Babban Sakataren Ma’aikatar Kimiyya […]
Gwamnatin Tarayya ta ce, kamfanonin masaku na bukatar garambawul cikin gaggawa saboda inganta karin abin da Najeriya ke samarwa a shekara (GDP).
A yayin taron kungiyar masu bincike na masaku ta Najeriya (TRAN) na duniya karo na 6, Ministan Kimiyya da Fasaha Dokta Ogbonnaya Onu ya bayyana muhimmancin garambawul ga masakun.
Babban Sakataren Ma’aikatar Kimiyya da Fasaha Mista Bitrus Bako Nabasu ne ya wakilci Dokta Onu inda ya bayyana rashin ingancin masakun kasar nan. “Akwai bukatar ma’aikatun gwamnati da hukumomin masu zaman kansu su bayar da tasu gudunmawar wajen yin garambawul ga masakun Najeriya,” inji shi.
Ministan ya ce, yanzu haka gwamnatin Muhammadu Buhari na kokarin inganta bangarorin masaku. “Abin takaici ne ganin yadda bangare masakun kasar nan ya yi kasa yayin da fannin na daya daga cikin masu habaka tattalin arziki a shekarun1980 inda ke samar da ayyukan yi a lokacin. Kuma bangaren yana samar da kudade sama da Naira biliyan 8.9 wanda yake wakiltar sama da kashi 20 cikin 100 na kididdigar abin da Najeriya ke samarwa a shekara (GDP). Wannan ke nuna yadda mulkin Buhari ke mayar da hankali a kan farfado da masaku,” inji shi.
A jawabin bude taron Darakta Janar na Hukumar Bincike Albarkatun Kasa (RMRDC), Dokta Husaini Doko Ibrahim, ya ce bangaren masaku zai iya samar wa ’yan Najeriya dubu 700 ayyukan yi.
Ya kuma ce, bangaren zai taimaka wa kasar da kashi 25 cikin 100 na abin da kasar take samar wa a shekara (GDP) idan an yi wa bangaren garambawul.
Ibrahim ya ce, idan har ana bukatar yi wa bangaren garambawul sai masu fada aji a harkar sun sanya duk abin ake bukata a kamfanonin masakun kasar don a samu sauyi mai inganci.