‘bangaren shari’a da ’yan sanda suka jawo mutum dubu 36 ke zaman jiran shari’a a gidajen yarin kasar nan’

Hukumar Gidajen Yari ta kasa (NPS) ta sake zargin ’yan sanda da bangaren shari’a kan cushewar gidajen kurkuku a kasar nan.Kakakin Hukumar Gidajen Yari ta Najeriya Mista Ope Fatinikum wanda ya ce yanzu haka akwai mutum dubu 36 da 870 da suke zaman jiran shari’a a gidajen yarin kasar nan, ya yi wannan zargi ne […]

‘bangaren shari’a da ’yan sanda suka jawo mutum dubu 36 ke zaman jiran shari’a a gidajen yarin kasar nan’
‘bangaren shari’a da ’yan sanda suka jawo mutum dubu 36 ke zaman jiran shari’a a gidajen yarin kasar nan’

Hukumar Gidajen Yari ta kasa (NPS) ta sake zargin ’yan sanda da bangaren shari’a kan cushewar gidajen kurkuku a kasar nan.
Kakakin Hukumar Gidajen Yari ta Najeriya Mista Ope Fatinikum wanda ya ce yanzu haka akwai mutum dubu 36 da 870 da suke zaman jiran shari’a a gidajen yarin kasar nan, ya yi wannan zargi ne a ranar Talatar da ta gabata, lokacin da ya ziyarci hedkwatar Kamfanin Media Trust mai buga jaridun Trust da Aminiya da ke Abuja.
Mista Ope Fatinikum, ya ce dabi’ar gurfanar da wadanda ake zargi “a gaban kotu ba tare da wadatattun hujjoji ba da ’yan sanda ke yi” da kuma yawan “dage sauraren kararraki da bangaren shari’a ke yi, suna taimakawa wajen kara cinkoso a gidajen kurkukun kasar nan.
Ya ce wani lokaci sai a kai wanda ake zargi zaman jiran shari’a da niyyar za a kai shi kotu, “amma sai a iske alkalin bai halarci kotun ba,” inji shi.
Sai ya nuna rashin jin dadinsa kan yadda jaridar Daily Trust ta buga wani hoton wata motar daukar fursunoni da ta kasa a hanya, inda ya ce, bai kamata a sanya hoton a shafin gaba na jaridar ba, domin koda mota sabuwa ce tana iya samun matsala.