Bani da jari a wani kamfani a waje – Firaministan Birtaniya
Firaministan Birtaniya David Cameron ya ce ba shi da hannayen jari, ko kuxi a kamfanonin da aka kafa a wasu qasashen qetare.Kalaman na shi sun biyo bayan, bayanan da aka bankaxo daga kamfanin Mossack Fonseca, da suka nuna mahaifinsa da ya rasu, Ian Cameron, ya taimaka wajen tafiyar da wani kamfani a qasar waje, kamar […]
Firaministan Birtaniya David Cameron ya ce ba shi da hannayen jari, ko kuxi a kamfanonin da aka kafa a wasu qasashen qetare.
Kalaman na shi sun biyo bayan, bayanan da aka bankaxo daga kamfanin Mossack Fonseca, da suka nuna mahaifinsa da ya rasu, Ian Cameron, ya taimaka wajen tafiyar da wani kamfani a qasar waje, kamar yadda BBC ta bayyana.
An nemi ji daga Firayiminista Cameron, ko shi da kansa, ko kuma wani daga cikin iyalansa, ya amfana da kamfanin da mahaifin nasa ya tafiyar, ko kuma suna da niyyar amfana da shi nan gaba.
Shugaban jam’iyyar adawa ta Labour a Birtaniya ya yi kiran a gudanar da cikakken binciken biyan haraji, kan dukkan ‘yan qasar da aka ambato sunayen su a takardun na Panama.
Har ila yau, takardun sun ambato sunan wasu shugabanni da kuma fitattun mutane da hannu a badaqalar kamar su: Sarki Salman na Saudiyya da tsohon Sarkin Qatar, Sheikh Hamad bin Khalifa Al Thani da Shugaban Qasar Haxaxxiyyar Daular Arabawa (UAE) Khalifa bin Zayed da Shugaban Majalisar Dattawan Najeriya Dokta Bukola Saraki da fitattun ’yan wasan finan-finan Indiya kamarsu Amitabh Bachchan da Aishwarya Rai da kuma fitaccen xan wasan qwallon qafar nan xan qasar Argentina Lionel Messi da sauransu.
Hakazalika, a ranar Talata ne Firayiminstan qasar Iceland, Sigmundur Gunnlaugsson ya yi murabus, inda ya kasance shugaba na farko da kwarmata bayanai kaucewa biyan harin ta sa ya rasa muqaminsa.
Bayanan da aka kwarmata, sun nuna cewa Mista Gunnlaugsson da matar sa, sun mallaki wani kamfani a qasar waje mai suna, Wintris, alhalin bai bayyana hakan ga majalisar dokokin qasar ba.