Bankaɗa: Fitattun ’yan siyasa da ‘suka mallaki’ gidajen Naira tiriliya 1.49 a Dubai

Binciken ya gano cewa wasu gidajen na ’yan Nijeriya maza ne amma aka yi rajistarsu da sunayen mata.

Bankaɗa: Fitattun ’yan siyasa da ‘suka mallaki’ gidajen Naira tiriliya 1.49 a Dubai

A cikin shekara hudu, wasu ’yan siyasar Nijeriya da na kusa da su (PEPs), sun ninka zuba jarinsu a harkar gine¬gine a Dubai ta Hadaddiyar Daular Larabawa, kamar yadda binciken Jaridar BusinessDay ya bayyana, kuma jaridar Daily Trust ta Intanet ta ruwaito.

A ranar Litinin da ta gabata ce, jaridar ta ce, binciken wani bangare ne na “Fatahu Dubai,” wanda aka kwashe wata shida ana yi kan ƙaruwa da boyayyar kasuwar gine-gine da Ƙungiyar Bayar da Rahoto kan Tsararrun Laifuffuka da Almundahana (OCCRP) tare da kafafen watsa labarai fiye da 70 suka jagoranta. Kafar labarai ta Economy Post ce kadai daga Nijeriya aka ce ta shiga cikin shirin.

Jaridar ta ruwaito cewa zuwa shekarar 2020, gidaje 800 ne aka gano na ’yan siyasar Nijeriya ne ko masu alaƙa da su, amma bayan shekara hudu adadin ya haura zuwa 1,600

Game da darajar kudadensu, rahoton ya ce, zuwa shekarar 2020, darajar kudin gidajen da suka kai Dala miliyan 400 aka gano na ’yan siyasar Nijeriya ne ko masu alaƙa da su a birnin kasuwanci na Hadaddiyar Daular Larabawan, amma yanzu kudin ya ƙaru zuwa kusan Dala biliyan daya da kuma gine-gine 1,600.

Rahoton ya ruwaito cewa Sashen Bunƙasa Filaye na Dubai ya bayyana ’yan Nijeriya a matsayin na biyu a tsakanin ’yan ƙasashen waje da suka fi sayen gidaje, a bayan mutanen Indiya.

“Nazarin bayanai da BusinessDay ta yi ya gano cewa baya ga ’yan siyasa manyan jami’an tsaro da ma’aikatan gwamnati da mutanen da suke da alaƙa da gwamnati da iyalansu sun mallaki kashi 88 cikin 100 na gidajen da aka ce na ’yan Nijeriya ne da ke Dubai,” in ji jaridar.

Ta ƙara da cewa “Wuraren da gine-gine suke, galibi na masu ƙumbar susa ne da suka hada da Burj Khalifa, gini mafi tsawo a duniya; Marsa Dubai, Al Merkadh, Palm Jumeirah, Wadi Al Safa, Madinat Al Mataar da Nad Al Shiba First da sauransu.

“Binciken ya gano cewa wasu gidajen na ’yan Nijeriya maza ne amma aka yi rajistarsu da sunayen mata don bat-da-sawu,” in ji rahoton.

Jaridar ta ce rahoton ba yana nufin an samu wadanda suke da gine-ginen da laifi ba ne, domin babu wata shaida da ta nuna daidaikun mutanen sun sayi gidajen ne da kudin sata ko na jama’a.

A ƙasa ga jerin mutanen:

Atiku Abubakar

Yana da gida mai dakunan kwana uku da aka ƙiyasta kudinsa a kan Dala miliyan 1.23 (kimanin Naira biliyan daya da miliyan 783 da dubu 500) a yankin Palm Tower da ke Dubai.

’Yar Atiku mai shekara 23

Gida mai dakin kwana daya a Trade Centre Second, an ƙiyasta kudinsa a kan Dala dubu 104 da 135 (kimanin Naira miliyan 150 da dubu 995 da 750).

Sannan tana da wani gidan mai dakunan kwana biyu a Hadaeƙ Sheikh Mohammed Bin Rashid da aka ƙiyasta kudinsa a kan Dala dubu 289 da 305 da senti 75 (kimanin Naira miliyan 419 da dubu 493 da 337 da kwabo 5).

Lateef Fagbemi

Ministan Shari’a kuma Babban Lauyan Nijeriya ya mallaki ginin da ya kai Dala dubu 85 da 846 (kimanin Naira miliyan 124 da dubu 476 da 700) a Al Hebiah Third.

Nasir El-Rufa’i

Wani gida mai dakunan kwana hudu da aka ƙiyasta kudinsa a kan Dala dubu 193 da 84 (kimanin Naira miliyan 279 da dubu 971 da 800) a rukunin gidaje na Al Hebiah Third an gano na tsohon Gwamnan Jihar ta Kaduna ne.

Yusuf Datti Baba-Ahmed

Gidaje takwas da aka ƙiyasta kudinsu a kan Dala miliyan 2.28 (kimanin Naira biliyan uku da miliyan 306) ne aka gano na Mataimakin Ɗan Takarar Shugaban Ƙasa na Jam’iyyar LP, Mista Peter Obi, a zaben 2023 ne. Gidajen suna zababbun wurare kamar Burj Khalifa, Al Yelayiss, Al Barsha South Fourth da Town Sƙuare Safi 2.

Ifeanyi Uba

Wani gida da aka ƙiyasta kudinsa a kan Dala miliyan 1.13 (kimanin Naira biliyan daya da miliyan 638 da dubu 500) ne aka gano na Sanata Ifeanyi Uba ne.

Yayin da aka alƙanta gidaje takwas ga matarsa Uchenna Uba. Ba a bayyana kudinsu a fayil din ba, amma daya daga cikin gidajen (kamar fada) a Wadi Al Safa 7 ya kai Dala miliyan 1.13 kimanin Naira biliyan daya da miliyan 638 da dubu 500), yayin da sauran aka ƙiyasta kowanensu ya kai Dala dubu 294 da dubu 516 (kimanin Naira miliyan 427 da dubu 48 da 200).

Attahiru Bafarawa

Gidaje 7 da aka ƙiyasta kudinsu a kan Dala miliyan 1.48 (kimanin Naira biliyan 2 da miliyan 146) da kuma wani gida da ke Palm Jumeirah da aka ƙiyasta kudinsa a kan Dala 750,112 (kimanin Naira miliyan 105 da dubu 15 da 680) aka ce na matarsa ce.

Ahmed Marƙafi

Wani gida a Burj Khalifa da aka ƙiyasta kudinsa a kan Dala 822,016 (kimanin Naira biliyan daya da miliyan 191 da dubu 923 da 200) da aka gano na tsohon Gwamnan na Jihar Kaduna ne.

Tafa Balogun

Marigayi tsohon Sufeto Janar na ’Yan sandan Nijeriya an jingina shi da gidaje biyar a wurare da dama da suka hada da Marsa Dubai. Kudin gidajen ya haura Dala miliyan daya (kimanin Naira biliyan daya da miliyan 450)

Mbu Joseph

An gano wani gini da aka ce tshon Mataimakin Sufeto Janar din ne da ba a fadi kudinsa ba.

Ahmadu Ali

Wani gida da ba a bayyana ƙimar kudinsa ba an gano na tsohon Shugaban Jam’iyyar PDP ta Ƙasa ce, yayin da aka yi kudin daya gidan da aka jingina ga ’yarsa Khadijah Nneamaka Ali a kan Dala dubu 422 da 887 (kimanin Naira miliyan 613 da dubu 186 da 150).

Maina Maji Lawan

An gano gine-gine 11 cewa na tsohon Gwamnan Jihar Borno ne kuma tsohon sanata (ba a fadi kudinsu ba).

Ashe Ahmadu Muazu

Matar tsohon Gwamnan Jihar Bauchi kuma tsohon Shugaban PDP na Ƙasa ta mallaki gida a Hadaeƙ Sheikh Mohammed Bin Rashid, da aka ƙiyasta kudinsa a kan Dala miliyan 1.16 (kimanin Naira biliyan daya da miliyan 682).

Christabel Bentu

Wani mai tallafa wa tsohon Gwamnan Jihar Filato Joshua Dariye, ya mallaki gida (ba a fadi kudin ba).

Isa Mahmoud Nuhu

An gano wasu gidaje biyu na babban jami’in Kwastam din ne. Ɗaya daga ciki an ƙiyasta kudinsa a kan Dala 553,802 (kimanin Naira miliyan 803 da dubu 12 da 900).

Salisu Abdullahi Yushau

Gidaje biyu ne aka gano cewa na tsohon babban sojin saman ne (ba a fadi kudinsu ba).

Mohammed Sidi Sani

Wani gida a Marsa Dubai, da aka ƙiyasta kudinsa a kan Dala 590,807 (kimanin Naira miliyan 856 da dubu 670 da 150)ne, aka gano cewa na tsohon Darakta Janar na Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta Ƙasa (NEMA) ne, wanda aka sallama daga aiki a watan Afrilun 2023 tare da darakatocin hukumar bakwai.

Hadiza Ali Sheriff

Wani gini a Marsa Dubai da aka ƙiyasta kudinsa a kan Dala miliyan 3.093 (kimanin Naira biliyan hudu da miliyan 484 da dubu 850) ne aka ce na matar tsohon Gwamnan Jihar Borno ne.

Nenadi Usman

Kamfanin hada-hadar gidaje ne aka ce mallakin tsohuwar Ministar Kudi ta Nijeriya ce.

Bobboi Kaigama

An gano wani gida (da ba a fadi kudinsa ba cewa) mallakin tsohon jagoran ’yan ƙwadago ne wanda ya shugabanci Ƙungiyar Manyan Ma’aikata (TUC).

Jimoh Ibrahim

An jingina gidaje bakwai ga Sanatan mai wakiltar Ondo ta Kudu, (ba a fadi kudinsu ba).

Ike Ekweremadu

An jigina gidaje biyar ga tsohon Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawan da ke zaman kurkuku a Ingila, (ba a fadi kudinsu ba).

Orji Uzor Kalu

Shi ma tsohon Gwamnan Abiya kuma yanzu sanata yana da gida guda daya (ba a fadi kudinsa ba).

Jeremiah Useni

Tsohon Gwamnan Soji na Jihar Bendel, tsohon Ministan Birnin Tarayya, Abuja, Baba Mai Tuwo,kamar yadda ake kiransa, Jeremiah Useni an gano yana da gida gudadaya a Dubai, (ba a fadi kudinsa ba).

Osita Chidoka

Wani rukunin gidaje da aka ƙiyasta kudinsa a kan Dala dubu 101 da 793 da 37 (kimanin Naira 147 da dubu 600 da 386 da kwabo 50) da ke Jabal Ali First an gano na tsohon Ministan Sufurin Jiragen Sama ne.

Olisa Metuh

Wani rukunin gidaje aka jingina ga tsohon Kakakin PDP na Ƙasa, Olisa Metuh (ba a fadi kudinsa ba).

Abdulsalami Abubakar

Wani gida a Marsa Dubai an ce na tsohon Shugaban Ƙasa na Soji ne (ba a fadi kudinsa ba).

Hassan Arɗo Tukur

Wani gini da aka ƙiyasta kudinsa a kan Dala miliyan 1.025 (kimanin Nairabiliyan 1 da miliyan 486 da dubu 250) an ce na tsohon Babban Sakataren tsohon Shugaban Ƙasa Goodluck Jonathan ne.

Adeyemi Ikuforiji

Wani gida a Marsa Dubai an ce na tsohon Shugaban Majalisar Dokokin Jihar Legas ne (ba a fadi kudin ba).

Dan Etete

An ce akwai wani gida na Dan Etete (Dauzia Loya Etete), tsohon Ministan Man Fetur na Nijeriya ne (ba a fadin kudinsa ba).

A baya: Ban mallaki wani gida a wajen Kaduna ba — El-Rufa’i

Sai dai shekara guda kafin gudanar da wannan bincike, tsohon Gwamnan Jihar Kadunar, ya yi da’awar gidan da ya mallaka a duniya baki daya shi ne wanda yake Kaduna.

A tattaunawa da wani gidan rediyon jihar, El-Rufa’i ya ce bai wawuri kudin jihar zuwa Dubai ba, kuma ya  ƙalubalanci  magabatansa a jihar su rantse kan ba su saci dukiyar jihar ba.

Ya ce, “Ina farin ciki mun gina ingantattun hanyoyi da za su yi shekara da shekaru. Ba irin hanyoyin da suka gina a baya ba, wadanda bayan shekara biyu, bayan ruwan sama sau biyu, hanyoyin za su lalace.

“Akwai dimbin aiki a gabanmu. Burinmu muna so mu ga dukkan hanyoyin Kaduna sun zamo na kwalta ne. Duk wanda ya zo Kaduna ba zai ga hanyar laka ba.

“Mutane na iya gani mun yi wadannan ayyuka ne da bashin da muka ciyo. Ba mu warurin kudin muka kai Dubai muka sayi gidaje ba, ko muka je Jabi Road muka gina fadoji ba.

“Mu ba irin wadacan mutane ba ne. Na zama Gwamnan Jihar Kaduna ne ina da gida daya kacal da ke Titin Ɗanja a Unguwan Sarki, Kaduna.

“Na kammala wa’adin mulkina, alhamdulillah…wannan ne gidana kadai. Ba ni da wani gidan. Ban gina gidan ƙasaita ba. Kuma ba na buƙatarsa.”

El-Rufa’i bai mayar da martani ga binciken Jaridar BusinessDay ba, har zuwa lokacin haɗa wannnan rahoto.

Manoma 7 sun rasu a hatsarin mota a Minna

Farashin litar mai zai haura N1,000 kwana nan — IPMAN 

Mayaƙan Lakurawa 3 sun shiga hannu kan bayar da cin hancin N1.6m

Boko Haram ta ƙone coci da gidaje a Borno