Bankin Acces na neman zama jagoran bankunan Najeriya

A makon jiya ne Bankin Access ya sanar da cewa zai hade da Bankin Diamond, sannan bankin ya ce zuwa wata uku masu zuwa za a kammala hadakar wato a rubu’in farko na badi, duk da cewa da farko an yi ta samun kwan-gaba-kwan-baya kan batun. Shugaban Bankin Diamond, Mista Uzoma Dozie ya ce hadewar […]

Bankin Acces na neman zama jagoran bankunan Najeriya

Shugaban Bankin Access Herbert Wigwe

A makon jiya ne Bankin Access ya sanar da cewa zai hade da Bankin Diamond, sannan bankin ya ce zuwa wata uku masu zuwa za a kammala hadakar wato a rubu’in farko na badi, duk da cewa da farko an yi ta samun kwan-gaba-kwan-baya kan batun.

Shugaban Bankin Diamond, Mista Uzoma Dozie ya ce hadewar bankunan biyu za ta samar da babban banki da zai taimaka matuka ga al’ummar Najeriya da Nahiyar Afirka baki daya.

Hadewar za ta sanya bankin na Acces samun karfin jarin sama da Naira tiriliyan 6, wanda hakan zai zama ya fi kowane banki karfin jari a Najeriya.

Bankin zai iya zama bankin mafi girma wajen hada-hadar kudade a Najeriya, inda ake tsammanin samun hada-hadar kudade da zai kai kimanin Naira tiriliyan 4 a karshen shekara kamar yadda kafar labarai ta The Cable ta ruwaito. A yanzu haka Bankin Access ne na uku, inda yake hada-hadar kimanin Naira tiriliyan 2.47 a karshen sulusin bana.

Haka a bangaren riba, bayan hadakar bankin zai zama jagora a tsakanin bankunan Najeriya. Yanzu haka Bankin Access ya sanar da samun riba ta Naira biliyan 500 bana, shi kuma Bankin Diamond ya samu ribar Naira biliyan 190. Idan aka hada ribar bankunan biyu, za a samu ribar da ta fi na kowane banki a Najeriya.