Bankin Access ya ciyo bashin kudi domin tallafa wa kananan ’yan kasuwa
Bankin Access ya ciyo bashin Dala miliyan 162.5 wato kimanin Naira biliyan 58.5 da zimmar taimaka wa kananan ’yan kasuwa. Sakataren Bankin, Sunday Ekwochi ne ya bayyana haka a wata takarda da ya aike wa Kasuwar Zuba Jari ta Kasa (NSE) a ranar Talatar da ta gabata. Yawancin kanana da matsaikatan kasuwanci da sana’o’i suna […]
Bankin Access ya ciyo bashin Dala miliyan 162.5 wato kimanin Naira biliyan 58.5 da zimmar taimaka wa kananan ’yan kasuwa.
Sakataren Bankin, Sunday Ekwochi ne ya bayyana haka a wata takarda da ya aike wa Kasuwar Zuba Jari ta Kasa (NSE) a ranar Talatar da ta gabata.
Yawancin kanana da matsaikatan kasuwanci da sana’o’i suna durkushewa ne a Afirka saboda rashin samun tallafi ko rashin sanin yadda za iya samun tallafin.
Babban Jami’in Gudanarwa na Bankin, Herbert Wigwe ya ce, “Za mu fi ba bangaren habaka kanana da matsakaitan kasuwanci muhimmanci domin da yawa daga cikinsu suna samun koma baya ne saboda rashin jari.”
Bankin ya kara da cewa, za su shirya wani tsari ne na shekara biyar, wanda zai taimaka wajen saukake biyan bashin da kuma samar da ayyukan yi da kuma haba tattalin arzikin kasar baki daya.