Bankin CBN: A tausaya wa talakawa da Gwamnatin Najeriya

Hakika talakawan Najeriya sun kidima da jin dokar da Babban Bankin Babban Bankin Najeriya CBN ya kafa na cire naira 50 a kowane mu’amula da aka yi ta banki matukar kudin ya kai Naira dubu 1000 guda. To a gaskiya talakawan Najeriya suna kira ga Babban Bankin Najeriya dama Gwamnatin Tarayyar Najeriya da suma wannan […]

Bankin CBN: A tausaya wa talakawa da Gwamnatin Najeriya
Bankin CBN: A tausaya wa talakawa da Gwamnatin Najeriya

Hakika talakawan Najeriya sun kidima da jin dokar da Babban Bankin Babban Bankin Najeriya CBN ya kafa na cire naira 50 a kowane mu’amula da aka yi ta banki matukar kudin ya kai Naira dubu 1000 guda. To a gaskiya talakawan Najeriya suna kira ga Babban Bankin Najeriya dama Gwamnatin Tarayyar Najeriya da suma wannan dokar garanbawul kamar haka,
Da farako abin da ya kamata a yi shi ne, kamata ya yi ace duk wanda ya yi mu’amala da adadin kudin ya kai kamar dubu dari 100000, shi ne ya kamata a ce an cire masa wannan harajin, amma adadin dubu 1000 daya ta yi kadan idan muka yi la’akari da bakin talauci da sama da mutum miliyan 100 suke fama da shi kuma kashi 90 cikin 100 na wadanda suke mu’amala da adadin dubu 1000 talakawa ne.
Kuma ai babu adalci a ce wai da wanda ya tura dubu daya da wanda ya tura biliyan 100 caji daya za a yi musu?! Sam babu adalci a nan.
Kuma kamar yarda masana tattalin arziki suke zayyana mana a Najeriya, ai akwai hanyoyi sama da dari 100 da Gwamnatin Najeriya za ta iya bi, domin kara adadin kudin shigar ta, ba wai sai an sanya wannan harajin ba, kadan daga cikin hanyoyi sun hada da siyar da takardun kudi (gobernment bonds) da rage dogaro akan man fetur, a kuma koma ga noma da kiwo da tono ma’adinan da Allah ya wadata mu da su, saboda ta haka ne kawai gwamnati za ta kara adadin kudin shigar ta. Sannan za ta iya sanya haraji ga hanyoyin manya-manyan biranen Najeriya kamar Kano da Legas.
Daga karshen ina kira ga Gwamnatin Najeriya da ma Babban Bankin Najeriya (CBN) da su duba koken talakawan Najeriya a sassasauta musu wannan dokar saboda talakan Najeriya yana fama da abin zai ci nema a yanzu.
Daga Salim Abubakar Imam Jingir dalibi a tsangayar Nazarin Tattalin Arziki, a Jami’ar Musulunci da ke Katsina, kuma Shugaban kungiyar Muryar Talaka reshen Jihar Filato 08067922200. [email protected].

’Yan bindiga sun kashe ’yan banga sun sace mai unguwa a Kaduna

A wata 19 Tinubu ya ciyo bashin tiriliyan 50

Jami’an Sibil Difens sun kashe mayaƙan Boko Haram 50

Sojoji sun kashe ’yan Boko Haram 30 a Borno