Bankin CBN ya amince bankuna su cire wani kaso lokacin ajiya ko cire kudi

Babban Bankin Najeriya (CBN) ya  amince wa bankuna su rika cire wani kaso na kudaden da jama’a suka ajiye ko suka cire daga ajiye daga asusun ajiyansu. A sabon tsarin kamar yadda takardar Daraktar Sashen Biyan Kudade na Bankin CBN, Sam Okojere ya sany awa hannu, za a caji kashi uku na abin da mutum […]

Bankin CBN ya amince bankuna su cire wani kaso lokacin ajiya ko cire kudi

Godwin Emefiele, Gwamnan Babban Bakin Najeriya (CBN).

Babban Bankin Najeriya (CBN) ya  amince wa bankuna su rika cire wani kaso na kudaden da jama’a suka ajiye ko suka cire daga ajiye daga asusun ajiyansu.

A sabon tsarin kamar yadda takardar Daraktar Sashen Biyan Kudade na Bankin CBN, Sam Okojere ya sany awa hannu, za a caji kashi uku na abin da mutum zai cire, sannan a ciaji kashi biyu na adadin abin da mutum ya ajiye idan kudin suka kai Naira dubu 500, a asusun daidaikun mutane.

A asusun ajiya na kamfanoni kuma, za a cire kudaden ne idan kudin ya kai Naira miliyan 3.

Sannan sanarwar ta nuna an fara aiwatar da sabon tsarin a jihohin Legas da Ogun da Kano da Abia da Anambra da Ribas da Babban Birnin Tarayya Abuja a shekaranjiya Laraba.

“Daga ranar 17 ga Satumban bana, Babban Bankin Najeriya (CBN) ya amince bankuna su fara cire kashi  biyu na kudin da za a jiye da kuma kashi uku idan za a cire idan kudin sun kai  Naira dubu 500 na daidaikun mutane, ko miliyan 3 idan kamfani ne,” inji sanarwar.