Bankin CBN ya kashe Dala biliyan tara don kare darajar Naira a watanni bakwai

Wani bincike da Aminiya ta gudanar ya gano Babban Bankin Najeriya na CBN ya sayar da Dala biliyan tara ga masu canjin kudin kasashen waje ta bankunan kasar a ranar 21 ga watan Fabarairu da ranar 31 ga watan Agusta shekarar 2017. Aminiya ta gano jimillar kudin ne bayan da ta tattara kididdigar ciniki wanda […]

Bankin CBN ya kashe Dala biliyan tara don kare darajar Naira a watanni bakwai

Wani bincike da Aminiya ta gudanar ya gano Babban Bankin Najeriya na CBN ya sayar da Dala biliyan tara ga masu canjin kudin kasashen waje ta bankunan kasar a ranar 21 ga watan Fabarairu da ranar 31 ga watan Agusta shekarar 2017.
Aminiya ta gano jimillar kudin ne bayan da ta tattara kididdigar ciniki wanda Babban Bankin ya fitar a tsakanin lokacin.
Cinikayyar ta Babban Bankin Najeriyar ta auku ne don samar da Dalar ga masu tafiye-tafiye da balaguron neman magani a kasashen waje da kudin makaranta da sauran harkokin da gwamnati ta amince da su.
A tsakanin lokacin, Bankin CBN ya rika zuba Daloli a kasuwar musayar kudin yayin da darajar naira ta fadi inda aka rika canjin Dala daya Naira 500.