Bankin CBN ya yi hasashen ajiye Dala biliyan 50 kafin karshen shekara
Babban Bankin Najeriya na CBN ya ce yana sa ran ya bunkasa ajiyar rarar kudin kasar da ke ketare zuwa Dala biliyan 50 kafin karshen shekarar 2018. Gwamnan Babban Bankin, Mista Godwin Emefele shi ne ya yi hasashen a taron karawa juna sani kan sha’anin kudi ga manema labarai da kuma editocin kasuwanci karo […]
Babban Bankin Najeriya na CBN ya ce yana sa ran ya bunkasa ajiyar rarar kudin kasar da ke ketare zuwa Dala biliyan 50 kafin karshen shekarar 2018.
Gwamnan Babban Bankin, Mista Godwin Emefele shi ne ya yi hasashen a taron karawa juna sani kan sha’anin kudi ga manema labarai da kuma editocin kasuwanci karo na 25 da bankin ya shirya a garin Uyo da ke jihar Akwa Ibom.
Emefele wanda Mataimakin Gwamna Mai Kula da Ayyuka, Mista Edward Adamu ya wakilta ya ce “Ajiyar kasar za ta ci gaba da bunkasa biyo bayan karuwar da aka samu a kwanannan. Rarar ajiyar za ta iya kai wa Dala biliyan 50 kafin karshen shekarar nan”.