Bankin Duniya ya ba Nijar tallafin biliyan 214

Ana sa tallafin noman zai sa Nijar ta noma wadataccen abinci a cikin gida da na fitarwa ketare

Bankin Duniya ya ba Nijar tallafin biliyan 214

Bankin Duniya ya amince ya bai wa Jamhuriyar Nijar tallafin CFA biliyan 214 domin bunkasa fannin noma da kiwo a kasar.

Tallafin ya kai Dalar Amurka miliyan 350 na zuwa ne a daidai lokacin da farashin kayan abinci yake ci gaba da tashin gwauron zabi.

Saboda haka ya yi hasashen bayar da tallafin a bangaren noma zai taimaka wajen samar da wadataccen abinci a kasar.

Ana kuma kyautata zaton tallafin za sa bayan samuwar wadataccen abinci a kasar, a samu rarar da za a fitar kasashen waje domin samun kudaden shiga.

Hakan zai taimaka wajen bunkasa tattalin arzikin kasar da ke fama da matsalar karancin abinci da ta tsadar rayuwa.

Kashi 40 kudaden Jamhuriyar Nijar na zuwa ne daga bangaren noma, a cewar bankin.

Ya kara da cewa kashi 80 cikin 100 na al’ummar kasar sun dogara ne da fannin noma domin samun kudaden shiga.