Bankin Duniya zai tallafa don farfado da madatsar ruwa ta Tiga

Bankin Duniya na shirin bayar da tallafin kudi domin farfado da madatsar ruwa ta Tiga, daa daga cikin manan madatsun da ke samar da ruwa da kuma shirin noman rani a Jihar Kano.Madatsar ruwan ta Tiga tana karkashin Ma’aikatar Albarkatun Ruwa ta kasa ne bisa kular Hukumar KogIN Hadeja-Jama’are, inda a yanzu haka take bukatar […]

Bankin Duniya zai tallafa don farfado da madatsar ruwa ta Tiga
Bankin Duniya zai tallafa don farfado da madatsar ruwa ta Tiga

Bankin Duniya na shirin bayar da tallafin kudi domin farfado da madatsar ruwa ta Tiga, daa daga cikin manan madatsun da ke samar da ruwa da kuma shirin noman rani a Jihar Kano.
Madatsar ruwan ta Tiga tana karkashin Ma’aikatar Albarkatun Ruwa ta kasa ne bisa kular Hukumar KogIN Hadeja-Jama’are, inda a yanzu haka take bukatar tallafi don magance matsalolin da suka dabaibaye ta.
Daraktar Bankin a Najeriya, Miss Francoise Nelly ce ta bayyana haka a yayin da ta jagoranci jami’anta bisa rakiyar jami’an ma’aikatar ruwa ta kasa, don ganin matsalolin da madatsar ke fuskanta. Ta ce “A shirye muke mu yi aiki da Hukumar Kogin Hadeja-Jama’are da gwamnatin Jihar Kano don farfado da wannan muhimmiyar madatsar ruwa.”
Ta ce bankin kuma zai bayar da irin wannan tallafin ga madatsun ruwa na Bakalori da ke Jihar Sakkwato da na Zobe da ke Jihar Katsina da tawagar suka ziyarta.
Daraktan Sashin Madatsun Ruwa da Noman Rani na Ma’aikaar Ruwa ta Tarayya, Mista A.R. Oyewole, ya ce sun je jihar ce da jami’an Bankin Duniya domin su gane wa idonsu irin nasarorin da aikin noman rani na Kano ya cimma tare da duba bangaren da za a tallafa wa shirin.”
Daraktan gudanarwa na Hukumar Kogin Hadeja-Jama’are, Alhaji Abdu dahiru kuwa cewa ya yi an gina madatsar ne shekara 40 da suka gabata kuma yanzu haka manoma dubu 42 da 500 ne suke amfana da ita a duk shekara. Ya ce sakamakon katsalandar da ciyawar Kacala da cikewar magudanan ruwa ke yi, an yi asarar eka dubu bakwai daga eka dubu 22 na fadin madatsar.