Bankin Duniya zai tallafa wa makiyaya wajen samar da madara don kasuwanci
Shugaban Kwamitin Bunkasa Sarrafa Amfanin Gona na Bankin Duniya, (Task Team Leader, World Bank), kuma jagoran Shirin Bunkasa Noma da Kiwo da Adana Abinci da Inganta Rayuwa, (APPEALS), Dokta Adetunji Oredipe ya ce, Bankin Duniya zai taimaka wa makiyaya Fulani da ke kauyen Dorayi a Zariya ta yadda za su inganta tatsar madara daga lita […]
Shugaban Kwamitin Bunkasa Sarrafa Amfanin Gona na Bankin Duniya, (Task Team Leader, World Bank), kuma jagoran Shirin Bunkasa Noma da Kiwo da Adana Abinci da Inganta Rayuwa, (APPEALS), Dokta Adetunji Oredipe ya ce, Bankin Duniya zai taimaka wa makiyaya Fulani da ke kauyen Dorayi a Zariya ta yadda za su inganta tatsar madara daga lita daya zuwa lita biyar a kowacce saniya.
Jami’in ya tabbatar da haka ne yayin wata ziyara da suka kai wa makiyaya a kauyen Dorayi da ke Karamar Hukumar Zariya a Jihar Kaduna.
Wannan aiki yana karkashin Shirin APPEALS ne.
Dokta Adetunji Oredipe ya ce dalilin ziyartar kauyen shi ne domin bunkasa hanyoyin da suke amfani da shi wajen samar da nono da nama zuwa na zamani don su bunkasa kasuwancinsu da ciyar da kasa gaba.
Babban jagoran ya ce, tuni suka fara koya wa makiyayan noman ciyawa da samar musu wurin da za su rika shayar da dabbobinsu ba tare da sai sun rika daukar dabbobin zuwa nesa ba ta yadda dabbobin suke sha wahala kafin su yi kiwo. Ya ce kuma hakan zai sa saniya ta huta ta yadda za ta tara madara da nama cikin sauki.
Daraktan ya ce, a cikin shirin akwai samar wa makiyaya kasuwar madarar da suke samarwa.
Bayan kammala ganawa da makiyayan ne ayarin ya ziyarci Kamfanin Madara na Saj Foods da ke Zariya domin kulla hulda kai0-tsaye da masu kiwo don samar da madara daga yankin Dorayi a Karamar Hukumar Zariya a Jihar Kaduna.
Da yake jawabi a lokacin da ya jagoranci ayarin, Shugaban APPEALS, Dokta Adejunji Oredipe wanda shi ne Babban jagoran tafiyar daga Abuja a karkashin shirin na Bankin Duniya zuwa Kamfanin Saj Foods da ke Marabar Gwanda a kan babban titin Zariya zuwa Kano ya bayyana gamsuwa da yadda ya ga harkokin ke tafiya a kamfanin.
Ya ce ’ya’yan kungiyar da ke wannan yanki za su samu dama tare da yin mu’ammala kai-tsaye da kamfanin a lokacin sayar da madarar da shanunsu suka samar.