Bankin Duniya zai tallafa wa manoman shinkafa a Jihar Neja
Hukumar Gudanarwa ta Bankin Duniya ta tanadar wa manoman shinkafa a Jihar Neja dala miliyan 200 a matsayin daya daga cikin matakan samar musu da kudin da za su yi amfani da su wurin bunkasa wannan aikin da yake da matukar tasiri, musamman yunkurin da Gwamnatin Tarayya ke yi na wadata jama’ar kasar nan da […]
Hukumar Gudanarwa ta Bankin Duniya ta tanadar wa manoman shinkafa a Jihar Neja dala miliyan 200 a matsayin daya daga cikin matakan samar musu da kudin da za su yi amfani da su wurin bunkasa wannan aikin da yake da matukar tasiri, musamman yunkurin da Gwamnatin Tarayya ke yi na wadata jama’ar kasar nan da shinkafa tare da hana shigo da ita daga kasashen ketare.
Hukumar ta ware wa manoman cin moriyar dala miliyan 20 daga cikin dala miliyan 200 da ta ware wa manoman shinkafa a jihohi 6 da suka hada da Legoa da Kano da Kogi. Sai jihohin da suka hada da Inugu da Anambra da Neja domin tabbatar da cewa wadannan rukunin manoman sun kara azamar yin noma a yankunansu, rani da damina.
Shugaban tawagar Bankin Duniya, Dokta Adetunji Oredipe ya shaida wa Gwamnan Jihar Neja, Alhaji Abubakar Sadik Sani Bello, irin moriya da kuma ribar da manoman shinkafar da ke jihar za su mora muddin gwamnatin jihar ta taka rawar da ta kamata na samar da Naira miliyan 96 a matsayin kasonta ga shirin na bunkasa noman shinkafa a fadin jihar.
Ya ci gaba da cewa: “Gwamnatin Jihar Neja ba ta samar da kasonta na shekarar na 2014, Naira miliyan 40 da kuma Naira miliyan 56 na shekarar 2015 ba. Don haka muddin gwamnatin ta samar da wadannan kudin, ko shakka babu za mu samar da kudaden, wadanda suna nan ajiye. Sai dai za a sa ido sosai domin tabbatar da cewa manoman ainihi ne za su ci moriyar shirin yadda ya kamata.” In ji shugaban.
Ya nuna cewa an fi bukatar wadannan manoman su kasance sun kafa kungiyoyin da za su fi jin dadin cin moriyar gagarumin shirin da aka tanadar wa jihohin da ke sassa daban-daban na Najeriya, sannan ana sa ran wannan za su rungumi shirin hannu bibiyu. Yin haka zai ba su damar noma shinkafa sosai tare da cin moriyar abin da suka sa a gaba, don za a tabbatar sun samu muhimman kayan aikin da suke bukata, domin sawwake musu wahalhalun da ke tattare da hidimar aikin.
Ya kuma bayyana cewa Allah Ya albarkaci Najeriya da kasar noma mai albarka, wadda muddin aka mayar da himma yadda ya kamata don kuwa bincike ya nuna akasarin manoman da ke aikin samar da shinkafa a kasar nan baki daya suna noma abin da bai taka kara ya karya ba.
Shugaban ya jaddada wa Gwamnan cewa a tsarin da Bankin Duniya ya gudanar, an yi tanadin akalla manoma dubu 317 ne za su ci moriyar shirin kai tsaye, sannan kuma suna sa ran akalla mutane fiye da miliyan daya da dubu dari hudu za su ci moriyar shirin ta wasu hanyoyin da za su sa shirin ya gudana yadda aka tsara, domin samun nasarar da aka sa a gaba.
Gwamnan Jihar Neja Alhaji Abubakar Sadik Sani Bello, wanda ya nuna farin ciki da ziyarar da aka kai musu, ya ce an yi ne a lokacin da ya dace kuma fannin noma a wannan zamanin yana taka muhimmiyar rawa wajen bunkasa fannin tattalin arzikin kowace kasa, bisa la’akari da yadda kasashe da dama suka samu kansu a mawuyacin halin rashin isassun kudi, domin gudanar da harkokin gwamnati ga jama’arsu.
Ya shaida wa tawagar Bankin Duniya cewa: “Ya zama dole kowace gwamnati ta yi nazarin hanyoyin samun kudin shigar da za ta yi amfani da su wajen gudanar da harkokin gwamnati da suka shafi samar wa jama’a muhimman ababen more rayuwa a duk inda suke, yadda aka yi musu alkawura lokacin da aka yi ta neman kuri’a. Wannan fannin zai samar wa miliyoyin jama’a ayyukan yi, ta haka kuma za a rage yawan marasa ayyukan yi cikin lokaci kankane.”
Gwamnan ya tabbatar wa tagawar cewa gwamnatinsa za ta gaggauta samar da kasonta na shekarun 2014 da 2015, domin su samu cin moriyar lamunin dala miliyan 20 da aka dade da kawar da kai daga cin moriyarsa. Bayan haka, gwamnatin za ta sake bin hanyoyin da suka kamata domin ganin yadda za ta ci moriyar wasu kudin da aka yi wa jihar tanadi domin samar wa manomanta.
Ya sanar cewa gwamnatinsa ba za ta yi kasa a gwiwa ba a duk lokacin da ta samu dama irin wannan, za ta yi amfani da ita yadda ya kamata. Wannan ne ya sa shi ganawa da Gwamnan Babban Bankin Najeriya, inda suka tattauna hanyoyin da za su bi domin jihar ta samu nata kason bunkasa ayyukan noma a fadin Jihar ba tare da wani bata lokaci ba.
Bugu da kari Gwamnan ya nuna cewa tuni suka fara tattaunawa da masu sha’awar zuba jari da kafa masana’antu, domin sarrafa albarkatun gona a sassa daban-daban na jihar. Don kuwa kowace shiyya a jihar tana da amfanin gonan da ta fi mayar da hankali a kai. Ya ce, mutanen shiyya ta daya wato kasar Nufawa, sun fi noma shinkafa da rake. Su kuma na shiyya ta biyu, Gwarawa sun fi noma doya da dawa da gero. Sai mutanen shiyya ta uku da suka fi mayar da hankali wurin noman gero da dawa da masara.
Ya bayyana takaicin ganin yadda aka yi watsi da kananan manoman da suka yi ta kokarin samar wa mutanen kasar nan kayan abincin da suke samun rufin asiri ba tare da sun samu wani tasarin da aka samar na kula da su yadda ya kamata ba. Ya danganta wannan sakacin da kasancewa daya daga cikin muhimman dalilan da suka sa matasa ke kyamar tsunduma aikin don yana tattare da kalubale da dama wadanda suka dade suna cin ma manoman tuwo a kwarya.
A nan Gwamnan ya ba Kwamishinan Ma’aikatar Kula da Albarkatun Noma da ya gaggauta zama da tawagar domin samar da hanyoyin da jihar za ta kara cin moriyar wasu shirye-shiryen da Bankin Duniya ta tanadar wa jihar. Sannan zai tabbatar Kwamishinan Kula da Harkokin Kudi ya samar da alkawarin da ya yi na samar da Naira miliyan 96 a matsayin daya daga cikin sharuddan samun dala miliyan 20.