Bankin First Bank ya saka wa kwastomominsa

Bankin First Bank ya sanar da cewa kwastomomin da ke mu’amala da shi sun ajiye kudin da ya kai Naira biliyan 800, inda hakan ya zama karo na farko a masana’antar bankunan kasar nan, sannan bankin ya yi alkawarin kawo sababbin hanyoyin saka wa kwastomominsa. Manajar da ke lura da kwastomomi na bankin, Misis Adebimpe […]

Bankin First Bank ya saka wa kwastomominsa
Bankin First Bank ya saka wa kwastomominsa

Bankin First Bank ya sanar da cewa kwastomomin da ke mu’amala da shi sun ajiye kudin da ya kai Naira biliyan 800, inda hakan ya zama karo na farko a masana’antar bankunan kasar nan, sannan bankin ya yi alkawarin kawo sababbin hanyoyin saka wa kwastomominsa.

Manajar da ke lura da kwastomomi na bankin, Misis Adebimpe Ihekuna, ta sanar da hakan a Legas a ranar Litinin a lokacin da ake bikin ba kwastomomin bankin kyaututtukan da suka lashe.
Don bankin ya nuna wa kwastomominsa jin dadinsa sakamakon kasancewarsu tare da shi ne ya ware Naira miliyan 500 don saka musu a tsawon shekara 6 da ta gaba wanda aka fara tun a shekarar 2008.
Wannan shi ne shiri karo na 6 da bankin yake yi don kwastomominsa, inda na wannan karon ya yi masa lakabin ‘FirstBank Sabings Bonanza’, kwastomomin sun lashe kyaututtukan ne ta hanyar ajiya a bankin.
Ihekuna ta bayyana an ware wa wannan shirin Naira miliyan 200 don bada kyaututtuka da za a ci gaba da ci.
Ihekuna ta ce: “Bankin ya kashe fiye da Naira miliyan 200 don sayan kyaututtuka da kuma kudin da aka ba kwastomomi. Kwastomomi 1,452 suka samu nasarar lashe kyaututtuka a wannan shiri na ‘FirstBank Sabings Bonanza’. Kowa ya sani an fara wannan shirin ne a watan Satumbar bara, inda aka kawo karshensa a yau Alhamis (makon jiya). Kwastomomi 6 sun samu nasarar lashe sabbin motoci kowannensu, inda kwastomomi 60 suka samu kyautar talabijin mai inci 32 kowannensu, wadansu 60 din suka lashe kyautar na’urar fitar da sauti (home theater), inda wadansu kwastomomi 60 suka samu Naira dubu 50 kowannensu.”
Ta bayyana bankin na amfani da ire-iren wadannan shirye-shiryen ne don cusa wa jama’a burin ajiyar kudi a banki.