Bankin GT ya aiyana ribar biliyan 200 a shekarar 2017
Bankin Guaranty Trust ya fitar da sakamakon hadahadar kudinsa na shekarar 2017 ga ’yan Najeriya da kuma cibiyar hadahadar hannun jari ta birnin Landan wanda ya nuna bankin ya samu riba kafin biyan haraji na Naira biliyan 200 da digo 2. Hakan yana nuna samun karuwar riba da ta kai ta kashi 21 da […]
Bankin Guaranty Trust ya fitar da sakamakon hadahadar kudinsa na shekarar 2017 ga ’yan Najeriya da kuma cibiyar hadahadar hannun jari ta birnin Landan wanda ya nuna bankin ya samu riba kafin biyan haraji na Naira biliyan 200 da digo 2.
Hakan yana nuna samun karuwar riba da ta kai ta kashi 21 da digo 13 cikin 100 a kan Naira biliyan165 da bankin ya samu a shekarar da ta gabata a watan Disamban shekarar 2016.
Wani nazari da wakilinmu ya yi kan sakamakon da bankin ya fitar ya nuna ya samu karin kashi daya da digo daya wato karin Naira biliyan 419 daga Naira 414 da ya samu a watan Disemban shekarar 2016.
Wannan ya hada da karuwar samun kudin ruwa da kuma kudin da bankin ke samu ta hadahadar da masu hulda da shi ke yi ta yanar Gizo.