Bankin IMF ya yi hasashen raguwar farashin mai a shekarar 2019
Bankin Duniya na IMF ya ce matsakaicin farashin gangar mai zai kasance Dala 62 da digo 31 a shekarar 2018 da kuma Dala 58 da digo 24 a shekarar 2019 kiuma zai ci gaba a haka har zuwa wani lokaci. A yanzu ana sayar da gangar danyen mai tsakanin Dala 65 zuwa Dala 70 […]
Bankin Duniya na IMF ya ce matsakaicin farashin gangar mai zai kasance Dala 62 da digo 31 a shekarar 2018 da kuma Dala 58 da digo 24 a shekarar 2019 kiuma zai ci gaba a haka har zuwa wani lokaci.
A yanzu ana sayar da gangar danyen mai tsakanin Dala 65 zuwa Dala 70 a kasuwar duniya.
Bankin duniyar ya sanar da haka ne a taron tattalin arziki da aka gudanar a birnin Washintan DC inda bankin ya yi hasashen bunkasar tattalin arziki da kashi daya da digo tara zuwa kashi biyu da digo daya cikin dari a shekarar 2018.
Bankin ya yi hasashen samun bunkasar tattalin arziki Najeriya da kashi daya da digo tara a shekarar 2019.