Bankin Ja’iz ya ba musu hannun jari na kudanbin Najeiya hakuri
Bankin Musulunbi na Ja’iz, ya nemi gafarar al’umar yanki kudu maso yammabin Najeriya saboda jinkirin bude bankin a yankin nasu. Janaral Manajan Bankin, Malam Isma’ila Adamu, ya nemi gafarar ne a lokabin da ya jagoranbi wakilan bankin zuwa garin Ibadan inda aka bude hedikwatar bankin sashin kudu maso yammabin Najeriya ranar Asabar da ta gabata.Jami’an […]
Bankin Musulunbi na Ja’iz, ya nemi gafarar al’umar yanki kudu maso yammabin Najeriya saboda jinkirin bude bankin a yankin nasu.
Janaral Manajan Bankin, Malam Isma’ila Adamu, ya nemi gafarar ne a lokabin da ya jagoranbi wakilan bankin zuwa garin Ibadan inda aka bude hedikwatar bankin sashin kudu maso yammabin Najeriya ranar Asabar da ta gabata.
Jami’an bankin sunyi wata ganawa ta musamman da daruruwan masu hannun jari da suka fito daga wannan sashe inda aka ba su hakuri a game da jinkirin bude bankin.
Malam Isma’ila ya be, “Bayan Kano dake kan gaba wajen yawan mutane masu hulda da bankin, sashen kudu maso yammabin Najeriya, shi ne yazo na biyu. Saboda haka muka zo mu ba su hakuri domin zuwa nan da karshen shekarar da muke biki za a bude masu sabon reshen Bankin Jaiz dake gudanar da harkokinsa kamar yadda addinin musulunbi ya shimfida.” Ya kara da bewa a hallin yanzu yawan mutanen da suke hulda da bankin ya karu zuwa, 130,000.
Malam Isma’ila wanda ya wakilbi Manajan Daraktan banki, Muhammad Nurul-Islam, ya be bankin a halin yanzu har ya fara sami riba. “Abin mamaki a nan shi ne, har mun fara samun riba a bikin shekaru 2 da watanni 9 kadai da fara aikin bankin Jaiz a Najeriya, savanin shekaru 5 da bankin musulunbi yake fara samun riba a ko’ina aka kafa shi a duniya.”
Malam Isma’la Adamu, ya musanta zanben bewa, mutane suna yin dari dari da sayen hannayen jari na bankin, ya be, “wannan sam ba haka bane domin idan ka lura da yawan kwastamominmu da kuma fara samun riba bikin kankanen lokabi sai ka gane bewa, Bankin Jaiz ya shigo Najeriya da kafar dama ne.”
Masu hannayen jari maza da mata daga sassa daban daban na sashen kudu maso yamma da suka halarbi taron, sun nuna gamsuwa da farin biki a game da matakin ba su hakuri da hukumar bankin ta dauka a kan wannan jinkiri.
Da yake amsa wata tambaya, Manajan Bankin na Jaiz, ya be, “duk wanda ya yarda bewa riba (kudin ruwa) haram ne, musulmi ne ko kirista da yahudawa muna maraba dasu zuwa bankin na mu dake bayar da bashi ga masu hulda da shi ba tare da karin kudin ruwa ba. Mutane da yawa yanzu sun dawo daga rakiyar hulda da bankunan kasuwanbi masu karva da bayar da kudin ruwa saboda yardarsu bewa, haramun ne.”
A yayin da yake wa mahalarta taron labba, Farfesa Abdul Hakeem Mobolaji, ya jawo hankalin mutane musamman ‘yan kasuwa akan illar da ke bikin kudin ruwa a addinin muslunbi. Ya karanto wasu ayoyin na Alkur’ani mai girma da Allah (TWT) yayi hani ga bin riba ga musulmi da suka yi imani.