Bankin Ja’iz ya fitar da masu taurin bashi daga kurkuku
Gidauniyar Bankin Ja’iz ta fitar da masu taurine bashi da ya kai su ga zaman kurkuku da ke tsare a gidan yarin Katsina.A ranar Litinin da ta gabata ne Bankin Ja’iz ya fitar da mutum shida daga gidan yarin Katsina da suke fama da matsalar da ta shafi gaza biyan bashin da ake bin su, […]
Gidauniyar Bankin Ja’iz ta fitar da masu taurine bashi da ya kai su ga zaman kurkuku da ke tsare a gidan yarin Katsina.
A ranar Litinin da ta gabata ne Bankin Ja’iz ya fitar da mutum shida daga gidan yarin Katsina da suke fama da matsalar da ta shafi gaza biyan bashin da ake bin su, kamar yadda Sakataren Gidauniyar Bankin na Ja’iz Alhaji Umar Farouk Yakubu wanda ya wakilci Babban Daraktan Bankin Ambasada Adamu Babangida ya ce, gidauniyar na biya wa masu irin wannan matsala ta gaza biyan bashin da ke kai su zama a gidajen yari.
“Mun lura da halin da jama’a suke ciki wadanda bashin da ake bin su kan kai su gidan yari saboda sun gaza biya. Wannan ne ya sa Ja’iz ya ga yana da kyau ya rika bin gidajen yari domin taimaka wa irin wadannan mutane da sauran wasu mabukatan da muka ga ya dace a taimaka musu,” inji shi.
Alhaji Umar Farouk ya ce, zuwa yanzu gidauniyar ta kashe sama da Naira miliyan shida a jihohin Kano da Kaduna da Katsina ga wadanda matsalar ba shi ta kai su ga zama gidan fursuna tun daga lokacin da bankin ya bullo da wannan tsari.
Da suke nuna farin cikinsu a kan wannan gudunmawa da gidauniyar bankin ke bayarwa, wasu daga cikin wadanda suka amfana, Lawal Sani da Jummai Abubakar sun gode wa gidauniyar da jami’an bankin tare da yin kira ga masu hannu da shuni da sauran al’umma su yi koyi da bankin. Har wayau, sun ja hankalin jama’a musamman ma’abuta cin bashi da masu bayarwa su rika kai zuciya nesa. “Masu cin bashi in ma ba su bar cin bashin ba, to su rika kokarin biya a cikin lokaci domin kauce wa fadawa cikin rikici. Su kuma wadanda suke bayar da bashi su rika yi wa wadanda suka ba bashin uzuri musamman a lokacin da suka tabbatar za a biya su,” inji su.
Sauran wadanda gidauniyar ta Ja’iz ta biya wa bashin sun hada da Safiya Uzairu da ake bi Naira dubu 45, sai Ibrahim Maibota, Naira dubu 30 da Lawal Sani, Naira dubu 87 da Jummai Abubakar, Naira dubu 49 da Usman Iliya, Naira dubu 70 sai kuma Umar Haruna, Naira 2500.