Bankin Sifen ya yi kuskuren sayar wa jariri hannun jari

Bankin Nobagalicia da ke kasar Spain ya yi kuskuren sayar wa jariri wata hudu hannun jarinsa, don haka kotu ta yanke masa hukuncin biyan diyyar. Kotun da ke Ponferrada, ta yanke cewa wannan cinikin haramtaccen ne, inda ta bayyana cewa, dole a dawo da Yuro dubu hudu da 800 na jarin daka zuba da sunanan […]

Bankin Sifen ya yi kuskuren sayar wa jariri hannun jari

Hedikwatar bankin NobagaliciaBankin Nobagalicia da ke kasar Spain ya yi kuskuren sayar wa jariri wata hudu hannun jarinsa, don haka kotu ta yanke masa hukuncin biyan diyyar. Kotun da ke Ponferrada, ta yanke cewa wannan cinikin haramtaccen ne, inda ta bayyana cewa, dole a dawo da Yuro dubu hudu da 800 na jarin daka zuba da sunanan iyayen jaririn, don biyan kudin da aka kashe wajen gudanar da shari’a.
Duk da cewa an yi cinikin hannun jarin ne da sunan iyayen jaririn, wanda ya mallaki hannun jarin an rubuta sunan jaririn ne. Kuma a kasar Spain haramun ne a sayar wa jariri hannun jari.
Bankin ya gabatar da cikakkun takardun da ke nuni da cika sharuddan ciniki, amma alkali ya yanke cewa babu hujja, kuma a cewarsa, babu ta yadda jariri ya fahimci hakikanin sarrafa dukiya ko hajar da ake sayarwa.

Ban zama Shugaban Kasa don na tara kuɗi ba — Tinubu

Babu buƙatar mu riƙa tsayar da motoci muna duba takardu — ’Yan sanda

‘Yan bindiga sun ƙone gidan mai da motoci 4 a Enugu

Kwalara ta kashe fiye da mutum 300 a Sudan