Bankin Sky ya tallafa wa gidan yara marasa galihu
Gidan yara marasa galihu da ke Unguwar Tudun Maliki a birnin Kano, ya samu tallafin kayayyakin dubban Naira daga bankin Sky Bank, domin saukaka rayuwar yaran da kula da jin dadinsu. A yayin da Manajan Shiyya na Bankin Skye, Alhaji Muntaka Badaru ya ce tallafin kayan da bankin ya bai wa gidan nakasassun na daya […]
Gidan yara marasa galihu da ke Unguwar Tudun Maliki a birnin Kano, ya samu tallafin kayayyakin dubban Naira daga bankin Sky Bank, domin saukaka rayuwar yaran da kula da jin dadinsu.
A yayin da Manajan Shiyya na Bankin Skye, Alhaji Muntaka Badaru ya ce tallafin kayan da bankin ya bai wa gidan nakasassun na daya daga irin ayyukan da suke gudanarwa, domin tallafa wa al’umma.
Ya ce tallafin da suka bayar aiki ne na wajibi a gare su, a maimakon aikin tausayawa. “Muna tabbatar da ’yancin dan Adam ga kowa, kuma an hore mu a kan taimako ba domin tausayawa kawai ba, sai domin sauke nauyi na wajibi, wannan ya sanya muka bayar da wadannan kayan tallafi na koyon karatu ga wannan cibiya.”
A jawabin manajan reshen bankin na titin Murtala da ke Kano, Mista Zaman Kalau, ya ce an shirya bayar da kayan tallafin ne don ya dace da dace da ranar yaki da jahilci ta duniya.
Shi a jawabinsa yayin karbar kayan a madadin cibiyar, Babban Daraktan Hukumar Kula da Manyan Makarantun Sakandare ta Jihar Kano, Alhaji Habibu Hassan El-Yakub, ya yaba wa hukumar bankin bisa tallafin da suka bayar, inda ya ce za a yi kyakkyawan amfani da kayan.