Bankin Sterling ya fadada harkokin bayar da bashinsa
Bankin Sterling ya fadada hanyar bayar da rancensa ta yanar gizo da ake kira Specta, inda yanzu daidaikun mutane da suke kananan kasuwanci za su iya cin moriyar shirin ba sai masu karbar albashi ba. Shugaban Sashen Harkokin Saye da Sayarwa na bankin, Mista Shina Atilola ne ya bayyana haka a wata sanarwa da ya […]
Bankin Sterling ya fadada hanyar bayar da rancensa ta yanar gizo da ake kira Specta, inda yanzu daidaikun mutane da suke kananan kasuwanci za su iya cin moriyar shirin ba sai masu karbar albashi ba.
Shugaban Sashen Harkokin Saye da Sayarwa na bankin, Mista Shina Atilola ne ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar a lokacin da bikin cika shekara daya da fara shirin Specta aLegas, inda ya ce sun fadada shirin domin manhajar na iya tantance masu neman bashi tare da ba su kudaden bayan amincewa.
Ya ce Bankin Sterling yana da burin mayar da shirin Specta ya kasance mafi sauri wajen samun bashin kudi domin tallafa wa kananan ’yan kasuwa da masu fara kasuwanci.
Ta take karin haske kan tsarin, Misis Benedicta Sadoh ta ce bankin ya bayar da bashin kimanin Naira biliyan 10 ga abokan hulda sama da dubu 11, sannan ya gabatar da musu da katin kudi da sauransu bara.
Sannan ta kara da cewa bankin zai bayar da kimanin Naira biliyan 40 ga kimanin abokan hulda dubu 50 bana.
Da yake amsa tambaya a kan yadda bankin zai bi wajen fadada shirin, sai Atilola ya ce za su yi amfani da kafofin sadarwa da sauransu.
Ita kuwa Sadoh ta kara da cewa dukan basussukan da bankin ya bayar ana amfani da su yadda ya kamata, sannan za a fara shirye-shiryen murnar cika shekara biyu da fara shirin, inda ta bayyana cewa duk wanda shiga shirin a tsakanin 4 da 14 ga watan Fabrailu zai samu bashin kan ribar kashi 1.29 cikin 100.
Shi dai tsarin Specta, wani tsari ne na bayar da rancen kudi har Naira miliyan 5 wanda ake yi a cikin minti biyar kawai ba tare da cike-ciken takardu ba ko wakili.
Rancen da ake bayarwa sun hada da daukar nauyin aure da biyan kudin gida da na karatu da lafiya da sauransu.