Bankin UBA ya yaba wa jaridun Daily Trust
Shugaban bankin United Bank for Africa wanda a takaice ake kira UBA, Dokta Toni Elumelu, ya yaba wa shugabanin kamfanin Media Trust da ke buga jaridun Daily Trust da Aminiya saboda kokarin da suke yi na gudanar da aikin jarida bisa tsari. Ya yi furucin ne yayin da shugaba kuma babban jami’i na kamfanin Media […]
Shugaban bankin United Bank for Africa wanda a takaice ake kira UBA, Dokta Toni Elumelu, ya yaba wa shugabanin kamfanin Media Trust da ke buga jaridun Daily Trust da Aminiya saboda kokarin da suke yi na gudanar da aikin jarida bisa tsari.
Ya yi furucin ne yayin da shugaba kuma babban jami’i na kamfanin Media Trust Nigeria Limited, Malam Kabiru A. Yusuf ya kai masa ziyara ofishinsa da ke Legas a ranar Talatar da ta gabata dangane da hadin gwiwar da bankin ke da shi da kamfanin jaridar. Bankin dai kan dauki nauyin taron karrama gwarazan Afirka duk shekara da kamafanin jaridar ke shiryawa.
Elumelu ya ce jaridar Daily Trust ta yi fice wajen kwarewa da kuma hangen nesa yayin da ta hada biyun wajen kirkiro da taron karrama ’yan Afrika shekara.
Ya bayyana cewa kamfaninsa na UBA zai ci gaba da hada gwiwa da Daily Trust don ci gaba da gudanar da taron tare da daga darajar nahiyar Afirka a idon duniya.
Malam Kabiru ya bayyana cewa kamfanin Media Trust ya kirkiro taron ne don ya karrama mutanen Afirka da suka yi fice wajen bayar da gudunmawarsu ga bunkasa da kuma ci gaban nahiyar baki daya.
Shugaban ya yaba da yadda bankin UBA yake bayar da hadin kai da gudunmawa ga nasarar taron da kuma karrama nahiyar Afirka.