Bankuna sun damfare mu biliyan 22 cikin wata guda – MTN
MTN ya ce kudaden nasa ne ba na masu ajiya ba
Kamfanin sadarwa na MTN ya yi zargin cewa wata guda bayan fito da tsarin biyan kudi na MOMO PSB, bankunan Najeriya sun damfare shi kudadeb da uska kai Naira biliyan 22.
A wata kara da kamfanin ya shigar da bankuna 18 a kasar nan, ya bayyana cewa sun karkatar da jimillar kudin ne, kwatankwacin Dalar Amurka miliyan 53.7 zuwa asusun ajiyar da abokan huldar bankunan ke kula da su a kasar.
- Najeriya ta shigo da danyen sukari na N410bn cikin shekara daya
- 2023: Har yanzu ina kokarin neman wanda zai min Mataimaki — Tinubu
A wata takardar sammacin mai kwanan watan 30 ga watan Mayun 2022 da wani Lauya Lotanna Chuka Okoli (SAN) ya aike wa bankuna 18, MOMO PSB na MTN na zargin cewa kudaden da aka karkatar nasa ne, ba na abokan cinikin bankunan ba.
Daga cikin bukatar kamfanin na MTN ya shigar, akwai neman kotu ta umurci bankunan 18 da su ba da lissafin kudaden da ke cikin asusun kwastomominsu da kuma kudaden da kwastomomin suka cire.
A wata takardar rantsuwar kotu, Shugaban gudanarwar MOMO PSB Ltd, Mista Anthony Usoro Usoro ya yi ikirarin cewa MOMO PSB Ltd ne mallakin jimillar kudi Naira biliyan 22.3 da ke ajiye a cikinta na hakika.
Ya kuma kara da cewa a ranar 24 ga watan Mayun 2022, sun lura da cewa an karkatar da kudade daga asusun ajiyarsa zuwa wasu asusu daban-daban da bankuna 18 ke kula da su.
Usoro ya ci gaba da cewa, an gudanar da hada-hadar kudi har 700,000 tare da shaidar shigar su cikin asusun ajiya daban-daban kimanin 8,000 a cikin bankuna 18 da aka lissafa.
Ya kara da cewa da gano faruwar lamarin, hukumar gudanarawar MOMO PSB Ltd ta rufe ayyukanta, domin takaita illar da hakan zai haifar, tare da tuntubar bankunan domin fara dawowa da su daga asusun ajiyar bankunan 18 daban-daban.
MOMO na zargin cewa, a karkashin dokar Babban Bankin Najeriya (CBN) kan tsarin tura kudade na gaggawa asusun bankuna mabambanta, karkashin sashe na 2 (D), da na 33 (1) 6), da na 47 (2) na kundin Babban Bankin na 2007, ya zama wajibi a kan bankunan su dawo da kudaden, tare da samar da sauran bayanan da MOMOn ya bukata.
Ya zuwa lokacin hada rahoton nan dai kotu bata sanya ranar fara sauraron karar ba.