Canjin Dala ya kai N750 a bankunan kasuwanci

Kwana biyar bayan dakatar da Gwamnan CBN, Godwin Emefiele, farashin da bankuna ke bayar da canjin Dala yakan kai N750.

Canjin Dala ya kai N750 a bankunan kasuwanci

‘Yan canji na kokawa da matakin CBN
Hoto:
REUTERS

Kwana biyar bayan dakatar da Gwamnan Babban Najeriya (CBN), Godwin Emefiele, farashin da bankuna ke bayar da canjin Dala yakan kai Naira 750.

Aminiya ta gano cewa bayan Shugaba Tinubu ya dakatar da Emefiele ne CBN ya sakar wa bankunan kasuwanci marar sayar da Dala gwargwadon yadda kasuwa ta kama.

Majiyoyi da dama daga ’yan kasuwa sun shaida wa Aminiya cewa a halin yanzu farashin da bankuna ke ba su canjin Dala yakan kai Naira 750.

Hakan kuwa na zuwa ne kwanaki bayan rahoton Aminiya da ke cewa bankin CBN ya kara karya darajar Naira.

Idan ba a manta ba, a jawabin fara aikin Shubaga Bola Tinubu ya yi alkawarin daidaita farashin canji, ta yadda zai zama na bai-daya a bankuna da wurin ’yan canji.

Binciken wakilinmu ya gano cewa a halin yanzu bankuna na iya ba da canjin kudaden kasashen waje gwargwadon yadda kasuwa ta kama, lamarin da ke nufin harkar canji ta zama marar kaidi a Najeriya.

Masu sharhi dai na lura da yadda abubuwa ke gudana a kasuwar ta canjin, inda suke jiran fitowar alkaluma domin tabbatar da hakikanin halin da ake ciki.

Kawo yanzu dai babu wani bayani ko tabbaci daga CBN, kasancewar kokarinmu na ji daga bankin ya ci tura.

Ana dai sa ran zuwa yau da yamma bankin zai fitar da sanarwar da za ta fayyace halin da ake ciki.

’Yan bindiga sun sace Farfesa, sun nemi N10m kuɗin fansa

Za a ɗauke wutar lantarki na tsawon mako 2 a Abuja

Hukumar tace fina-finai ta dakatar da Samha kan shigar banza

Sakataren Gwamnatin Ondo ya rasu bayan yin hatsarin mota