Bankuna sun fara fallasa miloniyoyi masu taurin bashi
A farkon makon nan ne bankunan kasar nan da suka hada da bankin Union da Sterling da Enterprise da Skye da Zenith da Unity suka buga sunayen masu taurin bashi kamar yadda Babban Bankin Najeriya ya bukace su.Babban Bankin Najeriya ne ya ba da umarni ga bankunan wata uku daga watan Mayu zuwa Yuli ga […]

A farkon makon nan ne bankunan kasar nan da suka hada da bankin Union da Sterling da Enterprise da Skye da Zenith da Unity suka buga sunayen masu taurin bashi kamar yadda Babban Bankin Najeriya ya bukace su.
Babban Bankin Najeriya ne ya ba da umarni ga bankunan wata uku daga watan Mayu zuwa Yuli ga duk wanda ya ci bashin banki ya biya ko kuma a fallasa sunansa da kamfaninsa. Sauran bankunan da ba su bayyana masu taurin bashin ba, sun ce za su buga nasu masu taurin bashin idan suka kammala hada sunayensu, saboda wasu sun fara rage bashin da ake bin su daf da za su saki sunan masu taurin bashin a jaridu.
Manyan masu kudi da ke mazurai tare da nuna sumui lumui suke, suna cikin masu rububin mayar da kudin da suka karba bashi bayan a baya sun dauka sun ci bulus.
Wani ma’akacin banki da bai so a ambaci sunansa ba ya ce wadanda ba su fara biya ba, wato masu kunnen kashi an fara fitar da sunayensu a ran Litinin da ta gabata.
Bugu da kari duk wanda aka rubuta sunanasa a bakin littafin masu kin biyan bashi, to za a hana shi shiga hada-hadar hannun jari da duk wata harka ta kudi. Kuma za a ci gaba da fallasa duk wanda ya ci bashi ya shekara bai biya ba.
A bankin Union mutum shida daga cikin mutum 176 sun karbi bashin Naira biliyan 27 da miliyan 910, kuma sun hada da kamfanin harkokin mai da iskar gas na Dec Oil & Gas da ake bi Naira biliyan 15 da miliyan 700 wanda ya ranci kudin domin yin kwangila a 1999 zuwa 2000, masu kamfanin su ne Patrick Ugboma da Pius U. Malaka.
Sai kuma kamfanin Alliance Energy da shi ma ke harkar mai, da ake bi bashin Naira biliyan 4 da miliyan 920, kuma kamfanin ya karbi bashin ne tun 2004 da niyyar za a biya a shekarar 2006. Masu kamfanin su ne Akinwale Omoboriowo da Kojo Anan dan tsohon Babban Sakataren Majalisar dinkin Duniya Mista Kofi Anan da kuma Timi Austen-Peters.
Kamfanin Gine-gine na Hajaig Construction ana bin sa bashin Naira biliyan 2 da miliyan 990, bashin da aka bayar tun shekarar 2012 kuma lokacin biya ya wuce tun shekarar 2014. Masu kamfanin su ne Abdul Nasser Hajaig da Rud Wan Hajaig da Mohammed Hajaig. Sai Kamfanin Sapta International Industries Limited ana bin sa bashin Naira biliyan 1 da miliyan 870 kuma ya karbi bashin ne tun a 1987 kuma ya kamata ya biya a 1988. Daraktocin kamfanin su ne Aled Aloy Nwokodikwa da Clement Nwokodikwa.
Kamfanin Petroleum Project International ya hantari bashin banki na Naira biliyan 1 da miliyan 250 da aka karba tun shekarar 2004 da ya dace a biya a shekarar 2007. Daraktocin su ne Akinwale Omoboriowo da Kojo Anan da Timi Austen-Peters. Kamfanin Best Aluminum an bint sa Naira biliyan 1 da miliyan 110 don kudin fito da haya tun shekarar 2010 har 2012. Daraktocin sun hada da Cif Godwin Nweke da Cif Pius Nweke.
A Bankin Fidelity wadanda ke da taurin bashi sun hada da kamfanin wayar salula mai suna Starcomms da ake bi bashin Naira biliyan 3 da miliyan 80 har kashi uku. Na farko an karba ne a shekarar 2009 da ya kamata ya biya a shekarar 2014, na biyu shi ne Naira biliyan 1 da miliyan 680 da ya karba a shekarar 2011 da niyyar cewa zai biya a shekarar 2014, sannan aka sake kara masa bashin Naira biliyan 1 da miliyan160. Na uku kuma shi ne wanda aka ba shi a shekarar 2007 da burin zai biya a shekarar 2014. Daraktocin kamfanin su ne Cif Maan Lababidi da Paul Edwards daTajudeen dantata da Omar Lababidi da Dokta Chris Ogbechie da Olusola Oladokun. Bankin ya fitar da sunan masu taurin bashi 28. Sauran sun hada da Kesio Associates da ake bin sa Naira miliyan 328 da dubu 100 da kuma Diesel Solutions Naira miliyan 324 da dubu 280 da kuma Patem Global Limited da ake bi bashin Naira miliyan 268 da dubu 500.
Bankin Sterling shi ma yana bin masu taurin bashi da dama da suka hada da Sterling Kasolute Nigeria Limited da ya hantari bashin Naira miliyan 475 da dubu 300 a 1999 da niyyar biya a shekarar 2000. Sai Kamfanin Just Jays Limited da bankin ki bi bashin Naira miliyan 254 da dubu 700; sai kamfanin Alcun Industries Limited Naira miliyan 192 da dubu 100. Sai G.Cyrus Global Resources da ake bi Naira miliyan 187.
Kamfanin Harhada Manyan Motoci da ke Kano, wato -National Truck Manufacturers inda Sunil Pathanani da Alhaji Ibrahim Bayero suke daraktoci ya karbi bashi Naira miliyan 728 da dubu 230 a watan Afrilun 2008 da ya kamata a biya a Yunin 2009.
Sai kamfanin Nadabo Energy Limited, wanda ya karbi bashi daga bankin Enterprise da ya kai Naira biliyan 1 da miliyan 550 a Fabrairun 2008 da ya kamata a biya a Oktoban 2013, daraktocin kamfanin sun hada da Sanata Nuhu Aliyu da Cif Dabid Ajobola Olorunleke da Ali Jeldi Abubakar-Peters.
A Bankin Zenith, kamfanin Energy Company Nigeria mai daraktocin da suka hada da A. Abidoye Ayoola da Ojeifo Musa da Grant Gilbert Temisan da Oji Theophilus Ifeanyichukwu da Manjo Janar Nom Yunana mai ritaya da Ayoola Oluwole, ya ci bashin Naira miliyan 743 da ya gaza biya a kan lokaci.
Wani ma’aikacin banki da bai son a fadi sunansa ya ce Babban Bankin Najeriya ya hana a tona sunan wadanda ya kai kara kotu game da batun don a girmama shari’a.
Wani Babban Lauyan Najeriya Cif Ajibola Aribisala (SAN), ya ce zai yi wuya a fallasa hakikanin sunan masu taurin bashin, domin wasu shafaffu ne da mai ko kuma akan yi ’yar gida da rub-da-ciki don a cuci jama’a da bankunan.
Shi kuwa shugaban Kamfanin Hada-hadar Hannun Jari mai suna APT Securities, Alhaji Kasimu Garba Kurfi ya shaida wa Aminiya cewa Babban Bankin Najeriya ya ja kafa wajen ceto bankunan kasar nan daga matsalloli da kuma barazanar durkushewa. Ya ce shi ya sa aka kafa Hukumar Kula da Hannayen Jari da Kaddarori da ake kira AMCON.
Sai a ganin wani tsohon ma’aikacin banki kuma masanin tattalin arziki, Alhaji Shu’aibu Idris Mikati, ya ce fallasa sunan masu taurin bashin banki a jaridu ba shi ne mafita ba. Ya ce domin hakan zai rage kimar bankunan kasar nan, saboda masu mu’amala da banki za su daina karbar bashin banki don gudun terere. Ya kuma ce wasu na da niyyar biya, amma idan sun sa gidansu ko wata kaddara a kasuwa don sayarwa a biya bashin in ba a saya ba, yaya za su yi?