Bankuna sun kori ma’ikata 110 saboda badakalar biliyan 182

An aikata almundahanar ce a tsakanin shekaru biyu

Bankuna sun kori ma’ikata 110 saboda badakalar biliyan 182

Bankuna

Akalla manya da kananan ma’aikatan bankuna 110 ne suka rasa ayyukansu cikin shekaru biyu, saboda laifuffuka masu alaka da damfarar abokan huldarsu.

Hakan dai na kunshe ne a cikin wani rahoton Cibiyar Bayar da Horo Kan Hada-hadar Kudi mai taken “Rahoton ayyukan damfara daga shekara ta 2021 zuwa 2023.

Mambobin cibiyar dai sun haɗa da kwamitin bankuna na Najeriya wanda ya kunshi Babban Bankin Najeriya (CBN) da Hukumar Kula da Bankuna (NDIC) da dukkan bankunan kasuwanci na Najeriya.

A tsawon wa’adin dai, lokacin da aka fi korar ma’aikata shi ne watanni uku na tsakiyar 2022, inda aka kori ma’aikata 20.

Kazalika, jimillar Naira biliyan 18.01 ne suka salwanta sanadiyyar almundahanar ma’aikatan da abokan hadin bakinsu, daga cikin biliyan 81.68 da aka yi harkallarsu a tsawon lokacin.

Ɗan shekara 60 ya rasu a hatsarin kwalekwale a Sakkwato

Yadda gobara ta ƙone kasuwar babura a Zamfara

Mun fara binciken turmutsutsin tallafin abinci — Shugaban ’Yan Sanda

Tinubu ya soke ayyukansa saboda rasuwar mutane a Abuja da Anambra