Bankuna za su fara cirar 0.5% daga masu tura kudi ta intanet

Bankin CBN ya umarci bankun su fara cirar wannan haraji nan da makonni biyu masu zuwa

Bankuna za su fara cirar 0.5% daga masu tura kudi ta intanet

Ginin Hedikwatar Babban Bankin Najeriya

Babban Bankin Najeriya (CBN) ya umurci bankunan kasar su fara cirar kaso 0.5 cikin 100 na duk kuɗin da aka tura ta intanet a matsayin harajin tsaron kudade ta kafar.

Sanarawar da daraktan kula da tsarin biyan kuɗi Chibuzor Efobi da kuma Daraktan tsare-tsaren na kuɗi Haruna Mustafa suka sa wa hannu ta ce bankuna za su fara zarar wannan kuɗi nan da makonni biyu.

An gabatar da wannan daftarin ga bankunan kasuwanci da kamfanoni masu hada-hadar biyan kuɗi da dangoginsu.

Sanarwa ta bayyana cewa an cimma wannan matsaya ce bayan la’akari da bukatar tabbatar da kudirin dokar yaƙi da satar kuɗi ta intanet ta shekarar 2015.

A cewar CBN,  harajin wani yunkurine na tabbatar da dokar inganta tsaron hada-hadar kuɗi ta intanet da aka amince da ita 2024.

Sanarwar ta ce, “Za a fara zarar wannan haraji ne a nan da makonni biyu  daga ranar da aka fitar da wannan sanarwa (6 ga Mayu, 2024).”

Sanarwar ta dauke wannan haraji a kan wasu kudaden da aka tura kamar haka:

  1. Albashi da fansho.
  2. Karbar rance ko biyan sa.
  3. Kudaden makaranta da dangoginsa
  4. Kudaden tallafi
  5. Kudaden kungiyoyin jinkai da na agaji
  6. Tura kudi tsakanin kwastomomin banki guda.
  7. Tura kudi tsakanin asusun mutum guda, ko da a bankuna daban-daban ne.
  8. Tura kudi tsakanin asusun aiki na cikin gigan banki
  9. Kudaden da bankuna ke tura wa CBN da wanda CBN ke tura musu.

Gobarar tankar mai ta yi ajalin mutum 18 a Enugu

An yi taron Maulidin ƙasa duk da gargaɗin harin ’yan ta’adda a Kano

An saki Falasɗinawa 200 da ke ɗaure a Isra’ila

Tinubu zai tafi taron makamashi a Tanzania