Bankwana: Buhari ya rantsar da sabbin kwamishinoni 7 a RMAFC

Shugaba Buhari ya rantsar da sabbin kwamishinoni 5 na Hukumar Tsara Alashi, kwana bakwai kafin ya sauka daga mulki

Bankwana: Buhari ya rantsar da sabbin kwamishinoni 7 a RMAFC

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya rantsar da sabbin kwamishinoni kasa bakwai a Hukumar Tsara Alashi ta Kasa (RMAFC), kwana biyar kafin ya sauka daga mulki

Buhari ya ba su rantsuwar aiki ne gabanin fara taron Majalisar Zartarwa ta Kasa ta karshe a gwamnatinsa a ranar Laraba, a Fadar Shugaban Kasa.

Sabbin Kwamishinonin da aka rantsar su ne: Hawa Aliyu daga Jihar Jigawa da  Rekiya Haruna (Kebbi) da Ismaila Agaka (Kwara) da Sanata Ayogu Eze (Enugu) da kuma Peter Opara (Imo).

Sauran su ne Kolawole Abimbola daga Jihar Oyo, sai kuma Ayuba Ngako daga Yankin Babban Birnin Tarayya.

A yayin zaman, Mataimakin Shugaban Kasa Yemi Osinbajo ya mika rahoton kwamitin da ya jagoranta kan inganta bangaren lafiya, domin samar da jadawali da nagartaccen tsarin kula da lafiya ga daukacin ’yan kasa cikin sauki.

Daga cikin shawarwarin kwamitin akwai batun kara kudaden da ake ba wa bangaren daga kashi 10 cikin 100.

Tinubu ya yi naɗin sabbin muƙamai huɗu

Majalisar Zartarwa ta amince da kusan Naira tiriliyan 50 Kasafin Kuɗin 2025

Tinubu ya jagoranci zaman Majalisar Zartarwa

HOTUNA: Ana shirye-shiryen jana’izar marigayi Lagbaja