Bankwana da ‘Azizu dan makaranta’
Wakar Marigayi Alhaji Yusuf Ladan kan yadda Uwani ta rika kewar masoyinta Azizu, wani yaro dan makaranta.
Tausa kalangunka
Nababa ka ji batun ’yar nan
Tana kiran mai kaunar ta.
Sai wata rana
Azizu sai ka dawo
Na tuno da ran bankwananmu
Azizu Dan makaranta…
- Dan Iyan Zazzau Alhaji Yusuf Ladan ya rasu
- Sakon mahaifinmu kwana daya kafin rasuwarsa —Ibrahim Balarabe Musa
Farin wata tun farko
Farin wata kwana goma
Habibu mun bankwana.
Kwana bakwai ban barci ba
Ina tunanin soyayya
Habibu Dan makaranta…
Na zama kurma
Azizu, na zama kurma
Ko saurayi dan wane ne
In yai kira ba na ji
Azizu sai ka dawo.
A yanzu ko ni na warke
Kunnuwana sun bude
Na ji kira har na waiga
Azizu sai ka dawo.
Wadannan baituka na wakar soyayya ce wacce marigayi Alhaji Yusuf Ladan ya kirkira a cikin shekarun farko bayan samun ’yancin kai a Najeriya a lokacin da yake aikin rediyo a Broadcasting Company of Northern Nigeria a Kaduna.
Satin da ya wuce Allah Ya yi masa rasuwa yana Dan Iyan Zazzau, Hakimin Kabala, Kaduna bayan ya yi ritaya. Allah Ya jikan sa.
Da ya rubuta wakar kusan shekara sittin da suka wuce, sai ya nemo marigayiya Uwani Zakirai da maikalangu Nababa da ’yan mata masu amshi suka rera ta cikin murya da salo da kida masu matukar dadi, abin da ya sa wakar ta kasance cikin jiga-jigan wakokin asali a Kasar Hausa.
Wakar ta ba mu labarin yadda Uwani – mawakiyar – ta rika kewar masoyinta Azizu, wani yaro dan makaranta.
Ta ba mu labarin saduwarsu ta karshe da bankwanan da ta yi da shi a dandalin wasan garinsu, daren da farin wata ke kwana goma.
Ta fada mana yadda tunanin Azizu ya hana ta ci da sha har ta kai ga ta rame, ta yi baki, ba saurayin da zai kira ta ta saurare shi saboda muhallin Habibu a zuciyarta.
A karshe ta fada mana alwashin da ta dauka na idan ba Habibu ba rijiya, ko ta shiga yawon dandi zuwa Badun ko Legas.
Kowace Uwani da nata Azizun’
Duk da cewa wakar Habibu Dan makaranta kirkirar ta aka yi, gaskiyar magana ita ce shekara sittin da suka wuce akwai “Uwani” da “Azizu” da yawa a kowane gari ko kauye da ilimin zamani ya isa gunsa a Arewacin Najeriaya.
Mutum ma zai iya cewa a lokacin kowace Uwani da nata Azizun.
A lokacin, mun taso a kauyuka, yara da ’yan mata tare muna abubuwa tare: zuwa kasuwa ne, da rafi a karshen mako, da wasa a dandali idan da farin wata ko lokacin bukuwan idi, da sauransu.
A cikin haka har soyayya da kauna ta fara shiga tsakanin yaro da yarinya tun kafin su balaga.
A lokacin, ’yan matan Kasar Hausa za su taru a dandali, su yi da’ira, kowacce na sako wakar masoyinta.
Idan ta yi nata, sai ’yar uwarta ta karba ta ci gaba, da haka har a gama kewayawa. Ga mai kalangu na kida, ga samari na kallo.
Sau da yawa, kowace yarinya na da nata taken da mai kalangu yake mata.
Ana zuwa kanta sai ya canza kida, ita kuwa ta cafe da waka cikin basira. Abin da ban sha’awa kwarai.
Wannan soyayyar farko ba a safai ake cin gajiyarta ba don ba za a jima ba yaron zai tafi makarantar gaba da firamare, wacce a lokacin makaratar kwana ce a wani garin nesa da masoyiyarsa. Ba za su hadu ba sai ya dawo hutu.
Ana haka, wata rana in ya dawo hutu sai ya samu an mata aure. Shi ke nan a bar shi da gyambon soyayyar da ba zai warke ba har abada.
Wani lokacin kuma har ya gama sakandare, ya tafi Turai karatun Diploma ko Digiri, ya bar masoyiyarsa a kauye.
A irin haka ne ita ma yarinyar za ta zauna cikin tunanin soyayyarsa har sai ya zo hutu, har lokacin da za a ce mata ta fitar da miji.
Dole ta fitar da wani cikin manyan samari wadanda sun isa yin aure, ta bar masoyinta wanda ya tafi makaranta nesa kuma bai wuce shekarunta ba balle a ce zai aure ta.
Alkawarin Uwani
Irin wannan halin ne Uwani ta samu kanta a ciki.
Azizu ya zauna mata a zuciya, ta ki hakura da soyayyarsa, ta ki yarda ta auri kowa, har sai ya dawo su yi aure. Ta rantse, ko Azizu, ko rijiya, ko dandi.
Alhaji Yusuf bai gaya mana Azizu ya dawo ba kafin Uwani ta yi aure.
Ya bar hikayar haka a rataye don mai sauraro ya yi tunanin me ya faru da Uwani.
Shin ta rike alkawarin soyayya cewa ba za ta auri wani banda Azizu ba a rayuwarta, ko ta saduda a karshe ta yi aure, ko kuma ta shiga dandi?
A wadannan shekarun kuruciya, soyayya ba yadda ba za ta yi da Uwani ba kuma ba inda ba zai kai ta ba.
Amma har karshen wakar, Azizu kam bai dawo ba.
Dr. Aliyu U. Tilde
11 Nuwamba 2020
Latsa nan ka saurari cikakkiyar wakar Habibu Dan makaranta