Bankwana da Ramadan (1440BH)
Watan Ramadana na bana ya zo ya wuce, inda aka gabatar da Sallar Idil Fitri a ranar Talata da ta gabata. BASHIR YAHUZA MALUMFASHI (08065576011) ya rubuta wannan wake da nufin bankwana da wannan muhimmin wata. Allah Ya maimaita mana, Ya amshi ibadojinmu, amin! Godiyarmu ga Allah Rabbana, Da ya ba mu zuwa Ramadana. […]
Watan Ramadana na bana ya zo ya wuce, inda aka gabatar da Sallar Idil Fitri a ranar Talata da ta gabata. BASHIR YAHUZA MALUMFASHI (08065576011) ya rubuta wannan wake da nufin bankwana da wannan muhimmin wata. Allah Ya maimaita mana, Ya amshi ibadojinmu, amin!
Godiyarmu ga Allah Rabbana,
Da ya ba mu zuwa Ramadana.
Jinjina naka wa Manzona,
Muhammadu Daha na Nana.
Tafiyar Ramadan ta cin mana,
Zango-zango mun murgina.
Mun sha yunwa mun dandana,
Mun ji kissa mun sha rana.
Ai ibada ce mara zanzana,
Bautar Allah mai zayyana.
Ruhinmu tsatsaf mun adana,
Wanke datti ko wani sofana.
Mun kaurace dukkan khiyana,
Matanmu ba mu ga shinshina.
Darasin tausai ya cin mana,
’Yan uwanmu riko da amana.
Sadaka kullum mun yanyana,
Ga fakirai za su su shanshana.
Rubi uku ne Ramadana,
Rahama, ceto, tsarin Rabbana.
Ga shi yau tafiyar ta auna,
Yau kamar an kyasta ashana.
Rabbana Allah kara mana,
Rahama, baiwa dado mana.
Ya Wahabu duk yafe mana,
Zunubanmu Ka kankare mana.
Ya Rahimu Ka yo duba nana,
Iyaye sunka jikan muna.
Ya Maliku Kai mulkinka na,
Shugaba ya zam gyaranmu na,
Ga kasarmu abin faharinmu na,
Lafiyarmu Allah Ka zayyana.
Bye-bye bye-bye Ramadana
Ni Bashiru yau na bayyana.