Banza ta kori wofi
Wani kwarto ne ya gane cewa mijin wacce yake so zai yi tafiya ranar wata Jumu’a. Dare na yi sai ya nufi dakin matar, ana kuwa hadari, saboda duhu ba ka ganin tafin hannunka. Ya shiga ya zauna, sun fara tadi sai matar ta ji muryar mijinta har ya kawo kofar daki. Ta duba ba […]
Wani kwarto ne ya gane cewa mijin wacce yake so zai yi tafiya ranar wata Jumu’a. Dare na yi sai ya nufi dakin matar, ana kuwa hadari, saboda duhu ba ka ganin tafin hannunka. Ya shiga ya zauna, sun fara tadi sai matar ta ji muryar mijinta har ya kawo kofar daki. Ta duba ba wurin buya sai ta ce wa kwarto ya kama maratayin jinkar dakin, watau kamar yana lilo, tun da kafafuwansa ba su taba kasa. Miji ya shigo ya zauna ya fara cin abinci, hannuwan kwarto suka yi sanyi, ya ji bai iya ci gaba da rikon maratayi, sai ya ce: “Na gaji.” Ita kuma matar sai ta ce: “Haba Nagaji, mijina na farko kai ka kashe shi, na biyu ma kai ka kashe shi, to don Allah ka bar mini wannan mana?” Miji ya yi zaton Nagaji wani aljani ne da ke kashe mazajen matar. Bai yi wata wata ba sai ya fantsama waje da gudu, shi kuma kwarto ya diro ya san inda dare ya yi masa.
Daga AbdulMajeed Umar Gummi, 08148888893